Ko makiyina bana fatan ya fada hannun yan bindiga – Mustapha Imam

Mustapha Imam daya daga cikin fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna da yan bindiga suka sace ya ce yana duba lafiyar yan bindigar lokacin da yake hannunsu.

A yaune dai yan bindigar suka samu damar sakin mutane biyar daga cikin mutanen da suke cigaba da garkuwa da su .

A wani fefan bidiyo da mutumin da ya jagoranci tattaunawar sakinsu, Mallam Tukur Mamu mawallafin jaridar Desert Herald ya fitar ya nuna Mustapha na cewa ko makiyinsa baya masa fatan shiga irin halin da suka samu kansu a hannun yan bindigar.

Imam wanda Farfesa ne a fannin likitanci a Jami’ar Usman Danfodiyo dake Sokoto ya ce yana kula da lafiyar yan bindigar da kuma sauran waɗanda aka kama.

More from this stream

Recomended