Gwamnatin Zamfara a arewa maso yammacin Najeriya ta ce ta kama masu kwarmata wa ƴan bindiga bayanai ‘informants’ fiye da 100 tun bayan katse layukan sadarwa a faɗin jihar.
Gwamnan Jihar Dr Bello Muhammad Matawalle ne ya bayyana haka cikin wata hira ta musamman da BBC a gidansa da ke Gusau babban birnin jihar.
“Toshe duk wata hanyar sadarwa tsakanin masu kwarmata bayanai ga ƴan bindiga ya yi tasiri sosai domin yanzu mun kama infoma fiye da 100,” in ji gwamna Matawalle.
Tsawon kwana 11 kenan da aka toshe layukan salula a fadin Zamfara, daga cikin matakan da hukumomi suka ɗauka na ƙoƙarin magance matsalolin taro a jihar.
Matakin toshe layukan na sadarwa ya shafi yankunan jihar Katsina da ke makwabtaka da jihar Zamfara.
(BBCHAUSA)