Kasuwar cinikin ‘yan ƙwallon ƙafa: Makomar Messi, Neymar, Mbappe, Bilic, Musiala, Ozil, Depay, Tomori, Seedorf

Lionel Messi

Fatan Paris St-Germain da Manchester City na ɗaukar Lionel Messi ya samu tagomashi bayan mutumin da ke takarar shugabancin Barcelona Emili Rousaud ya ce ba za su iya “ci gaba da biyan albashin” da suke bai wa ɗan wasan na Argentina daga bazara mai zuwa ba. (AS – in Spanish)

PSG ta shaida wa ma’aikatanta cewa su shirya domin za ta sayi Messi, mai shekara 33, daga Barcelona. (Football Transfers)

Rousaud yana son sake haɗa da Messi da ɗan wasan Paris St-Germain ɗan kasar Brazil Neymar a ƙungiyar ƙwallon ƙafar ta Sifaniya amma ya ce Barca ba za ta iya ɗauko ɗan wasan mai shekara 28 kafin kwangilarsa ta ƙare a 2022 ba. (AS – in Spanish)

Tsohon ɗan wasan Manchester City Pablo Zabaleta ya ce ƙungiyar ce “wurin mafi dacewa” da Messi zai koma idan ya bar Barca. (Stadium Astro, via Sun)

Akwai “matuƙar yiwuwa” Messi zai bar Barca domin ya tafi PSG a bazara mai zuwa, a yayin da ɗan wasan Faransa Kylian Mbappe, mai shekara 21, zai bar ƙungiyar ya tafi Real Madrid. (TalkSport)

West Brom na shirin korar kocinta Slaven Bilic sannan ta maye gurbinsa da tsohon kocin Ingila Sam Allardyce. (TalkSport)

Bayern Munich ta shirya sabunta kwangilar ɗan wasanta na tsakiya Jamal Musiala, mai shekara 17, inda zai riƙa karɓar £100,000 a duk mako a yayin da wasu ƙungiyoyin da ke buga gasar Firimiya ta Ingila suke ruguguwar ɗaukar ɗan wasan da ke buag gasar ‘yan ƙasa da shekara 21. (Mail)

Wakilin Mesut Ozil ya ce ɗan wasan na Jamus, mai shekara 32, yana son ci gaba da zama a Arsenal har sai kwangilarsa ta ƙare nan da wata shida – duk da cewa ƙungiyar tana so ya tafi a watan Janairu. (Tuttomercato – in Italian)

Paris St-Germain ta shirya tataunawa domin ɗauko ɗan wasan Lyon ɗan wasan ƙasar Faransa mai shekara 22 Houssem Aouar, wanda Arsenal ta so ɗauka a bazarar da ta wuce. (RMC Sport, via Sun)

Har yanzu ɗan wasan da Barcelona ta so ɗauka Memphis Depay, mai shekara 26, bai yanke shawara kan makomarsa ba, a yayin da kwangilar ɗan ƙasar Netherlands ke shirin ƙarewa a Lyon a bazara mai zuwa. (Goal)

Leeds United na saya ido kan ɗan wasan Chelsea ɗan ƙasar Ingila Fikayo Tomori, mai shekara 22, da zummar yin zawarcinsa a watan Janairu. (Football Insider)

Arsenal da Marseille na sha’awar ɗaukar ɗan wasan Portugal Fabio Vieira, mai shekara 20, daga Porto. (Record – in Portuguese)

More News

Yawan Mutanen Da Suka Mutu A Wutar Da Wani Matashi Ya Cinnawa Wani Masallaci A Kano Sun  Karu Zuwa 16

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce yawan mutanen da suka mutu sakamakon wutar da wani ya cinnawa wani masallaci a ƙauyen Gadan a...

An fara rushe wasu gine-gine 500 a kasuwar Karmo dake Abuja

Hukumar FCTA dake kula da birnin tarayya Abuja ta fara rushe gine-gine sama da 500 da aka yi ba bisa ka'ida ba a kasuwar...

Tinubu ya tarbi shugaban kasar Senegal Bassirou Faye a fadar Aso Rock Villa

A ranar Alhamis ne shugaba Bola Tinubu ya tarbi shugaban kasar Senegal Bassirou Faye a fadar Aso Rock Villa, a ziyarar da Faye ya...

NEMA ta karɓi ƴan Najeriya 150 da aka dawo dasu gida daga ƙasar Chad

Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Ƙasa NEMA ta ce ta karɓi ƴan Najeriya 150 da aka dawo da su bayan da su ka maƙale...