Hukumar Kididdiga ta Ƙasa wato NBS ta ce ƙarancin abinci, rashin tsaro tsadar farashi ya tilastawa gidaje da dama rage abincin da suke ci inda kaso 65 basa iya sayan abinci mai gina jiki saboda ƙarancin kuɗaɗe.
Hukumar ta bayyana haka ne cikin rahoton da ta fitar na tattara bayanan halin da magidanta su ke ciki.
An gudanar da binciken ne tare da haɗin gwiwar Bankin Duniya.
Rahoton ya ce ƙarin farashin kayan abinci da aka fi amfani da su ya shafi kaso 71 na magidanta yayin da ƙaranci abinci ya shafi sama da kaso uku na magidanta a shekarar da ta wuce.
Waɗannan ƙarancin sun fi ƙamari a watannin Yuni, Yuli da kuma Agusta abin da ya ƙara ta’azzara matsalar karancin abinci.
A wata hanya na jurewa yanayin kaso 48.8 na gidajen sun bayyana cewa sun rage yawan abinci da suke ciki.