Kasashen Musulmi sun yi tir da ƙona Alkur’ani a Sweden

Kasashen Musulmin duniya na ci gaba da yin tir da kona Alƙur’ani da masu fitowa zanga-zanga suka yi a kasar Sweden.

Kasar Maroko da ke Afirka ta yi wa jakadanta na can kiranye, sakamakon lamarin da ya faru

Wannan lamari dai ya faru ne a birnin Stockholm.

Ma’aikatar harkokin wajen kasar a birnin Rabat ta kira matakin a matsayin rashin da’a ga al’ummar musulmi, yayin da suke bikin Babbar Sallah.

Ministan harkokin wajen Turkiyya ya yi Allah-wadai da lamarin, inda ya ce wadanda suka shiya zanga-zangar na da hannu a abun da ya faru.

More from this stream

Recomended