
Hukumar NCDC dake yaki da cututtuka masu yaduwa ta sanar da samun kari mutane 84 da suka kamu da cutar Covid-19 da akafi sani da Coronavirusa jihohi 9.
NCDC ta sanar da haka ne cikin wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter ranar Asabar da daddare.
Rabe-raben mutanen da suka kamu da cutar ya nuna cewa jihar Lagos na kan gaba da mutane 33 sai jihar Borno mai mutane 18, Osun na da mutane 12, Katsina na da mutane 9 sai jihohin Kano da Ekiti da suke da mutane hur huɗu.
Har ila yau jihohin Edo da Bauchi na da mutane uku-uku sai jihar Imo da take da mutum guda.
Kawo yanzu mutane 1182 ne aka tabbatar sun kamu da cutar a Najeriya baki daya, mutane 222 cikinsu ne suka warke daga cutar.