Tsohon shugaban mulkin soja na Najeriya Janar Abdulsalami Abubakar (mai ritaya), ya yi gargadi kan kara farashin man fetur da cewa zai tura karin ‘yan kasar cikin fatara da talauci da mawuyacin hali.
Janar din ya bayyana haka ne a wurin taron tattaunawa na shekara-shekara karo na 19, wanda jaridar DailyTrust take shiryawa a Abuja

Tun a watan Nuwamba ne kwamitin wucin-gadi na majalisar tattalin arzikin kasar, karkashin jagorancin gwamnan jihar Kaduna Mallam Nasiru el-Rufa’i ne ya bayar da shawarar kara farashin mai.
Bisa ga dukkan alamu kuma nan da dan lokaci ne gwamnati za ta kara farashin man da ake sayarwa yanzu a yawancin sassan kasar a tsakanin naira 162 da 165 zuwa naira 302a kan kowace lita.
Tsohon shugaban ya ce yanayin tattalin arzikin kasar ya kara sa harkar tsaro ta tabarbarewa matuka
Rashin aikin yi har yanzu yana nan sosai, inda ake da ‘yan Najeriya sama da miliyan 18 da ke cikin fatara da talauci na ba gaira ba dalili. Ya ce duka wadannan sun taimaka wajen yin illa ga harkar tsaro.
Ya kara da cewa wannan yanayi hadi da illar da annobar korona ta haifar a duniya tare da matsalar barayin daji da ake fama da ita a jihohi da yawa a arewacin Najeriya, sun jefa kasar cikin gagarumar matsalar tsaro.
Janar Abdusalami ya ce: “Farashin kayan abinci na ci gaba da tashi ta yadda ‘yan Najeriya da yawa ba za su iya saye ba. Kuma kari a kan duka wadannan, ana sa ran kara farashin mai sosai a watannin da ke tafe kamar yadda gwamnati ta sanar a awatan Nuwamba da ya wuce. Dukkanmu mun sani idan haka ta kasance, za ta tura miliyoyin ‘yan Najeriya cikin fatara.”