Kanunfari na motsa sha’awa ga mata da maza da kuma jinkirta tsufa

kanunfari

Kanunfari fitaccen sinadari ne da galibin mutane ke amfani da shi wajen girki da sha da kuma wasu abubuwan na inganta lafiya da jin daÉ—i.

Ana amfani da itacensa ko ganyensa ko busasshe a sarrafa su domin biyan bukatu daban-daban a ko ina a faÉ—in duniya. Ko da yake galibin Larabawa ko al’ummar yankin Æ™asashen Asiya sun fi amfani da shi.

Sirrin shan ruwan kanumfari

Masana harkokin lafiya sun bayyana amfanin wannan sinadari na kanunfari a rayuwar dan adam.

A tattaunawarsa da BBC, wani likita a Najeriya Dr Ibrahim Badamasi, ya ce ruwan kanunfari na da amfani sosai ga lafiya saboda yana ƙunshe da sinadaran da ke yaƙi da cututtuka da bunƙasa garkuwar jiki. Ruwan kanunfari na taimakawa wajen saurin narkewar abinci da hana cutar ulcer. Yana taimakawa lafiyar haƙora da hana kumburin dadashi da fitar da jini.

Sannan ruwan kanunfari na taimakawa wajen rage ƙiba da teɓa. Yana maganin jiri da cutar kwalara. Sannan yana taimakawa wajen saisaita sukari a cikin jini da lafiyar hanta saboda yana ƙunshe da sinadaran da ke hana lalata ƙwayoyin halitta.

Amfanin kanunfari ga mata

Amfanin kanunfari ga mata da maza kusan guda ne. Binciken da masana kimiyya da dama suka yi ya nuna cewa kanunfari na Æ™ara wa mata da maza ni’ima. Kanunfari na da amfani ga mata wajen inganta Æ™wan haihuwa, sannan yana taimakawa wajen shawo kan matsalar rashin daukar ciki.

Kanunfari na bunÆ™asa isar wasu saÆ™onni ga Æ™waÆ™walwa waÉ—anda ke motsa sha’awa ga mata da kuma maza. Kanunfari na Æ™ara wa mata kuzari lokacin jima’i. Baya ga taimakawa wajen rage jiki yana sa rashin tsufa.

Man kanunfari na taimaka wa mata wajen samun sauÆ™in ciwon mara a lokacin al’ada da taÆ™aita kwanakin al’adar.

Amfanin kanunfari ga maza

Asalin hoton, MEDICALNEWS

Kanunfari na É—aya daga cikin magungunan gargajiya da ke Æ™ara wa maza lafiya domin kuwa yakan Æ™ara yawan sanadarin ‘testosterone’ wanda ke tasiri wajen haÉ“akar gaÉ“oÉ“in saduwa na namiji.

Rashin isasshen sanadarin ‘testosterone’ a jikin namiji na iya haifar masa da matsalar rashin Æ™arfin mazakuta, wanda kan rage masa Æ™arfin sha’awar saduwa.

Kanunfari kan inganta tafiyar maniyyin namiji. Yana kuma ɗauke da sanadarai da ke ƙara yawan maniyyin da namiji ke samarwa, wanda hakan shi ne abu mafi amfani ga lafiyar maza.

Bugu da ƙari kanunfari kan magance matsalar saurin fitar maniyyi ga namiji a lokacin saduwa, matsalar da ke yawan faruwa ga maza sanadiyyar gajiya ko kuma wasu matsaloli na daban.

Mai da ake samu daga kanunfari na Æ™ara Æ™arfin miÆ™ewar azzakari tare da inganta kwararar jini zuwa ga al’aura.

Ana amfani da kanunfari wajen magance saurin fitar maniyyi ga namiji a lokacin saduwa ne ta hanyar hada shi da wasu Æ™arin abubuwan, wadanda akan shafa a kan al’aurar namiji kafin saduwa.

Ga dai jeren abubuwa 8 da kanunfari ke yi a jikin É—an adam, daga Dr Badamasi

  • Yana kunshe da sindarai irin su Vitamin K da Fiber da Calories da carbs da Manganese
  • Yana kunshe da sindaran da ke hana lalata Æ™wayoyin halitta
  • Yana iya taimakawa wajen hana kamuwa da kansa ko sankara
  • Yana kashe kwayoyin cutuka
  • Yana inganta lafiyar hanta
  • Yana daidaita sukari a cikin jini
  • Yana Æ™ara lafiyar Æ™ashi
  • Yana hana kamuwa da ulcer

Adadin kanunfari da za a iya sha a rana guda

Masana kiwon lafiya sun ce mutane na amfani da kanunfari wajen hana saurin fitar maniyyi a lokacin saduwa. Ko daÉ—in jima’i. Sai dai ba a son shansa ko ci ya zarta iyaka. Idan aka yi amfani da shi sama da ka’ida yana iya illa sosai.

Ba a son a sha sama da itace hudu zuwa biyar a kowacce rana. Sannan ya dangata daga mutum zuwa mutum. Amma yana da kyau a tuntuɓi likita domin samun shawarwari yadda ya kamata a yi amfani da shi.

(BBC Hausa)

More News

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miÆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaÆ™i da yiwa tattalin arzikin Æ™asa ne ya hana shi bayyana...

Ƴan sanda sun kama mutane biyu dake samarwa ƴan fashin daji makamai a jihar Kaduna

Rundunar Æ´an sandan jihar Kaduna ta ce tana tsare da wasu mutane biyu da ake zargi da safarar bindiga a jihar. A wata sanarwa ranar...