Dubban masu zanga-zanga da suka fito a kungiyance domin yin Allah wadai da gina wani kamfani mallakar Aliko Dangote, sunyi karan batta da jami’an ‘yan sanda har ma suka tarwatsa su da hayaki mai sanya hawaye.
Acewar al’ummar garin Danmarke dake karamar hukumar Makoda a jihar kano ta bakin Ali Isah Thomas, yace “Ba suyi mamakin afkuwar wannan al’amari ba, saboda rashin kyakkyawar alakar dake tsakanin su da jagororin yankin wanda ba kasafai suke zama suyi mahawara dasu ba aduk lokacin da wani bakon al’amari ya taso don ciyar da su gaba.”
Isah Thomas ya kuma yi zargin cewa a yayin waccan fatattaka, ‘yan sandan sun harbi mutum biyu.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sadan Kano, DSP Abdullahi Haruna, ya karyata zargin harbi da masu zanga-zangar suka ce anyi, sai dai yace a kokarin da rundunar su tayi na ganin sun tseratar da rayuka da tabbatar da bin doka da oda, wannan yasa rundunar ‘yan sanda amfani da barkonon tsohuwa don tarwatsa masu zanga-zangar.
Wakilin Hausa7 Idris Usman Alhassan Rijiyarlemo ya nemi jin bahasi daga shugaban karamar hukumar Makoda Hon. Abubakar Salisu Makoda, don jin ta bakin sa game da zargin chefanar da filin ga Aliko Dangote don gina kamfani, kamar yadda masu zanga-zangar suka koka.
Sai dai har kawo lokacin da wakilin mu ya aiko mana da wannan rahoto bai sami jin ta bakin Hon. Makoda ba.