Wannan ita ce Rahaf Mohammed, budurwa ‘yar shekara 18 kuma ‘yar asalin k’asar Saudiyya da yanzu ta samu mafaka a k’asar Canada bayan ta tsere wa ‘yan’uwanta lokacin da suka je hutu a k’asar Kuwait.
Ta tsere ne kuwa ba don komai ba sai don RIDDA da ta yi, wanda laifi ne da hukuncinsa kisa ne a k’asashe irin su Saudiyya – inda ba a wasa da Shari’ar Musulunci. A cewarta, ana danne mata hakkokinta na ‘ya mace kuma tana matuk’kar fuskantar barazana sakamakon barin Musulunci da ta yi da kuma rashin amincewarta da wani auren zumunci da za a yi mata.
Bayan barinta Kuwait, ba ta tsaya a ko’ina ba sai a Birnin Bangkok na k’asar Thailand, inda daga nan ne ta yi niyyar cillawa Australia don neman mafaka. To sai dai hakan ya ci tura. A daidai wannan lokaci ne mahukuntan k’asar Thailand suka sassauta dokokinsu na ‘yan gudun hijira, har suka k’i mayar da ita inda ta fito – wato Kuwait – kafin daga nan a mayar da ita Saudiyya.
A bangkok ne ta samu kulawar Majalisar D’inkin Duniya har ta samu nasarar karb’uwa a k’asar Canada.
“…ni ce Rahaf Mohmed [sic], wacce nake neman mafaka a duk k’asar da za ta kare ni daga illa ko kisa da ‘yan’uwana za su min saboda na yi
Ridda,” a cewar Rahaf.
Allah sarki Rahaf! Allah Ya sa ki gane!
Muhammadu Sabiu ne ya rubuta wannan makala. Za a iya samunsa ta kafar Facebook: Muhammadu Sabiu