Esomnofu Ifechukwu daga makarantar Crown Grace, Mararaba, jihar Nasarawa, ya zama zakaran gasar Maltina Teacher of the Year karo na 10 a babban taron da aka gudanar a Legas a ranar Juma’a, 11 ga Oktoba, 2024.
Mr Ifechukwu, wanda aka zabe shi a matsayin Maltina Teacher of the Year na shekarar 2024, ya karɓi kyautar kuɗi har naira miliyan goma (₦10,000,000).
Bugu da ƙari, zai samu horo na ƙwarewa a ƙasashen waje da dukkanin kuɗaɗen tafiya, kuma za a gina masa kayayyakin more rayuwa na makaranta da darajar su ta kai naira miliyan talatin (₦30,000,000) a makarantarsa.
Kehinde Olukayode daga Molusi College, Oke-Sopen, Ijebu Igbo, jihar Ogun, ya zo na biyu, inda ya karɓi kyautar kuɗi ta naira miliyan uku (₦3,000,000), yayin da Aniefiok Udoh daga Community Secondary Commercial School, karamar hukumar Uyo, jihar Akwa Ibom, ya zo na uku, ya tafi gida da kyautar kuɗi ta naira miliyan biyu (₦2,000,000).
Haka zalika, wasu malamai 34 daga jihohin su daban-daban, waɗanda suka fito a matsayin zakarun jiha, kowanne ya samu kyautar kuɗi ta naira miliyan ɗaya (₦1,000,000).