Kalubalen La Liga da ke gaban Barcelona da Real Madrid a bana

Real Madrid Barcelona

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Barcelona da Real Madrid za su ci gaba da sa kwazo da zarar an ci gaba da gasar La Liga ta shekarar nan ba ‘yan kallo.

Cikin watan Maris aka dakatar da wasannin La Liga na 2019-20, saboda tsoron yada cutar korona.

Barcelona ta yi murna da Luis Suarez ya warke daga jinya da ya yi wanda tun farko ake tunani ya gama buga wasannin shekarar nan a raunin da ya yi cikin watan Janairu.

Eden Hazard ya warke ya kuma ci gaba da atisaye, hakan zai karkafa gwiwar Real Madrid wanda ya karya kafa a cikin watan Fabrairu.

Haka ma Marco Asensio ya ji sauki zai kuma taimakawa Karim Benzema a sauran wasannin da suka rage da Real Madrid za ta fafata.

Real Madrid za ta buga wasanta na gaba da Eiber ranar 14 ga watan Yuni a karawar ce Zinedine Zidane zai ja ragamar kungiyar wasa na 200.

Ita kuwa Barcelona za ta ziyarci Real Madrid ranar Asabar 13 ga watan Yuni.

Barcelona wadda take fatan cin kofin La Liga na uku a jere tana mataki na daya a kan teburin wasannin bana da tazarar maki biyu tsakaninta da Real Madrid.

Da yake ba ‘yan kallo za a ci gaba da gasar La Liga, Real za ta buga wasanninta na gida a filin Alfredo Di Stefano mai cin ‘yan kallo 6,000, bayan da ake gyare-gyaren Santiago Bernabeu.

Saura wasa 11 a karkare wasannin La Liga na bana da za a yi cikin mako biyar kuma watakila Barcelona tana da wasanni masu sauki nan gaba da za ta yi a gida da Athletic Bilbao da Atletico Madrid da wanda za ta je Sevilla da Villareal sune hudun da sai ta yi da gaske.

Real Madrid wadda ta ci Barcelona cikin watan Maris ta barar da damarta, bayan da Real Betis ta yi nasara a kanta, kuma tana da wasa biyar da ake ganin masu kalubale a wajenta da suka hada Valencia da Getafe da kuma Villarreal da za ta yi a gida.

Wadanda Real za ta yi a waje masu zafi kuwa sun hada da na Real Sociedad da kuma na Athletic Bilbao.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Wadanda ke kan gaba a cin kwallaye a gasar La Liga:

  1. Lionel Messi Barcelona 19
  2. Karim Benzema Real Madrid 14
  3. Lucas Perez Martinez Deportivo Alaves 11
  4. Gerard Moreno Villarreal CFVillarreal 11
  5. Roger Marti Salvador Levante 11
  6. Luis Suarez Barcelona 11
  7. Lucas Ocampos Sevilla FC 10
  8. Angel Getafe CF 10

More News

Peter Obi Ya Ziyarci Mutanen Da Su Ka Ƙone Sakamakon Wutar Da Wani Ya Cinnawa   Masallaci A Kano

Ɗan takarar shugaban ƙasa  a zaɓen 2023 ƙarƙashin jam'iyar Labour Party (LP) Peter Obi ya ziyarci mutanen da wani matashi ya cinnawa wuta a...

An sanar da zaman makoki na kwana biyar saboda mutuwar shugaban kasa a Iran

Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatollah Ali Khamenei ya sanar da zaman makoki na kwanaki biyar saboda rasuwar shugaban kasar Ibrahim Raisi...

Najeriya za ta dena shigo da man fetur a cikin watan Yuni – Dangote

Aliko Dangote mutumin da ya fi kowa arziki a Nahiyar Afirka ya ce Najeriya za ta daina shigo da man fetur a cikin watan...

An ceto mutane 9 daga wani ginin bene da ya ruguzo a jihar Niger

Mutane 9 aka samu nasarar cetowa daga wani ginin bene mai hawa ɗaya da ya ruguzo a yankin Sabon Gwari dake garin Minna babban...