Juyin mulkin Mali: Ecowas da sojojin kasar ‘sun cimma matsaya’

Anasa ran za a ci gaba da tattanawa ranar Litinin

Wakilan kungiyar kasashen kungiyar Yammacin Afirka, Ecowas, da mambobin rundunar sojin da ta yi juyin mulki a Mali sun amince da yarjejeniya kan batutuwa da dama, kwana guda bayan sun fara tattaunawa kan yadda kasar za ta koma kan turbar mulkin dimokradiyya.

Ana sa ran za a ci gaba da tattanawa ranar Litinin.

“Mun samu damar cimma matsaya kan batutuwa da dama ko da yake ba mu cimma matsaya kan komai da komai ba,” a cewar tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, wanda shi ne ke jagorantar sulhu tsakanin bangarorin biyu.

Shugabannin sojoji sun bayar da shawarar kafa gwamnatin rikon kwarya ta sojoji wacce za ta kwashe shekara uku tana “duba ginshikan kasar ta Mali”, a cewar kamfanin dillancin labarai na AFP wanda ya ambato rahotanni daga wakilan Ecowas.

Shugabannin sojojin sun kuma amince su saki shugaban kasar da suka yi wa juyin mulki Ibrahim Boubacar Keïta, in ji AFP.

Ecowas ta nanata kiran mayar da Mr Keïta kan mulki, sai dai dubban ‘yan kasar ta Mali sun fantsama kan titunan babban birnin kasar, Bamako, ranar Juma’a inda suka rika nuna goyon bayansu ga juyin mulkin.

Ƙarƙashin matsi, jagororin juyin-mulkin na da mabambantan ra’ayi

Mary Harper, Editan Afirka, BBC World Service

Sojojin da suka ƙwace mulki a Mali sun ce suna tattaunawa da jam’iyyun adawa da sauran ƙungiyoyi a ƙoƙarin kafa gwamnati.

Duk da irin kiraye-kiraye masu ƙarfi daga shugabannin yankin Afirka da ƙetare kan dawo da shugaban da aka hamɓarar Ibrahim Boubacar Keïta kujerarsa, wayanda suka jagoranci juyin-mulkin da ƴan adawa na nuna turjiya.

Suna son mahukunta da za su iya yaƙar rashawa, farfado da tattalin arziki da kawo ƙarshen ƙabilanci da rikicin jihadi.

Abin ya zo da mamaki, musamman ganin yadda ƙasashe duniya suka gaggara shiga tsakani domin kawo ƙarshen rikicin siyasar ƙasar.

More News

Gwamnan Kano ya sanya hannu kan dokar yin gwajin lafiya kafin aure

Gwamnan jihar Kano, Engr Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan wata doka za ta tilastawa masu yin aure yin wasu gwaje-gwajen lafiya gabanin...

An kashe kwamandan soji a Katsina

An kashe kwamandan sojoji na wani sansanin soji da ke Sabon Garin Dan’Ali a karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina a wani harin kwantan...

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...