Juyin mulki: An yanke alaƙar difulomasiyya tsakanin Nijar da Najeriya

Gwamnatin mulkin soja a Jamhuriyar Nijar ta yanke hulda da Najeriya bayan kokarin da kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS ta yi na warware rikicin shugabancin da kasar ke fama da shi.

An ruwaito cewa kungiyar ECOWAS ta bayar da wa’adin kwanaki bakwai ga gwamnatin mulkin soja ta mayar da hambararren shugaban kasar Mohamed Bazoum kan kujerarsa.

A ranar Alhamis ne shugaban Najeriya Bola Tinubu ya aike da wata tawaga mai karfi zuwa kasar domin ganawa da wadanda suka yi juyin mulki.

Sai dai jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa tawagar karkashin jagorancin Janar Abdulsalami Abubakar (rtd) ta gana da wakilan gwamnatin mulkin soja ne kawai, inda ta kara da cewa Nijar ta yanke hulda da Najeriya da Togo da Faransa da kuma Amurka.

“An kawo karshen ayyukan manyan jakadun Jamhuriyar Nijar” a kasashen Faransa da Najeriya da Togo da kuma Amurka,” in ji jaridar Rediyo Faransa ta nakalto daya daga cikin wadanda suka yi juyin mulkin a gidan talabijin na kasar.

More from this stream

Recomended