Joe Biden: Manyan kalubalen da sabon shugaban Amurka yake fuskanta daga kasashen Larabawa

  • Lyse Doucet
  • Chief international correspondent
Bayanan hoto,
Kungiyar ‘yan tawayen Houthi da ke kasar Yemen ta soki gwamnatin Trump bisa sanya ta a cikin kungiyoyin ‘yan ta’adda

“Jama’a, wannan wani lokacin ne na jarrabawa,” in ji sabon zababben shugaban Amurka lokacin da yake shan rantsuwar kama aiki ranar Laraba, tun kafin ya gama sauraren wadanne jarrabobi kasar take fuskanta shugaban ya kammala zancensa da cewa “rawar da Amurka za ta taka a duniya”.

Wasu daga cikin tambayoyin da za su yi wuyar amsawa su ne a kan lamuran Gabas ta Tsakiya.

Tsofaffin hannu ne suka fi yawa a cikin gwamnatin Joe Biden, mafi yawansu sun yi aiki da gwamnatin Obama, kums sun dawo domin su sake bibiyar tsofaffin matsalolin da ake fuskanta a baya.

Bayanan hoto,
Antony Blinken ya yi alkawarin tuntubar kawayen Amurka kafin ya sake shiga shirin tattaunawar Iran kan makamashin nukiliya

Manyan kalubalen da za su fuskanta sun hada da tsare-tsaren da a baya suka taimaka domin a aiwatar – a wuraren da al’amuran tsaro suka tabarbare a yanzu.

“Sun dauki darasi daga abubuwan da aka samu kuskure a cikinsu lokacin gwamnati Obama a Gabas ta Tsakiya,” in ji Kim Ghattas, jami’a a cibiyar kula da harkokin kasashen waje ta Carnegie Endowment for International Peace, kuma marubuciyar littafin “Black Wave” wanda ta yi kan rikicin Saudiyya da Iran a yankin Gabas ta Tsakiya. “Za su iya kallon abubuwan da ke faruwar ta wata mahangar ta daban, saboda sun san kuskuren da aka yi a baya, kuma yanzu yankin ya sauya ba kamar yadda suka san shi a baya ba.”

Manyan batutuwan da ke gaban wannan gwamnatin kan harkokin kasashen wajen sun hada da maganar Iran. Yarjejeniyar makamin nukiliya da aka cimma da kasashen duniya yanzu na cikin wani hali bayan da Donald Trump ya yi watsi da ita da kuma sanya wa Iran jerin takunkumi. Akwai mummunan yakin Yemen da ya yi kaca-kaca da kasar, wanda Obama ya goyi bayansa.

Bayanan hoto,
Donald Trump ya sha kare manufofin Yarima mai jiran gadon Saudiyya Mohammed bin Salman

Shugaba Trump ya fara gwamnatinsa da wani abu na daban, wanda shi ne zaben Saudiyya a matsayin kawa ta farko a watan Mayu a 2017, inda ya sanya hannu kan yarjejeniyar makamai ta dala biliyan 110 wanda shi ne ciniki mafi girma a tarihin Amurka. Hakan ya ba da dama ta tsara manufofi a kan Gabas ta Tsakiya tare da biyayya ga masarautar Saudiyya sannan da matsin lamba ga Iran.

“Kwararrun masana diflomasiyya kuma tsofaffin hannu da suka yi aiki da Obama lamarin yankin ke bukata,” in ji Hassan Hassan, editan mujallar Newslines, wadda ta mayar da hankali kan harkokin yankin.

Ya kara da cewa: “A ganin kasashen Larabawa za su iya shawo kan matsalar siyasar da ta addabi yankin ba tare da jagorancin Amurka ba. Amma bayan kusan shekara biyar da suka yi kokarin hakan, sun gano ba za su iya ba musamman a wuraren kamar Libya da Yemen da Iran har a ‘yar karamar kasar da ke makwabtaka Qatar.”

Bayanan hoto,
Majalaisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa yanke hulda da ‘yan tawayen Houthi zai iya jefa Yemen cikin matsalar fari

Mayar da hankali wurin jawo tsofaffin kawayen Amurka na daga cikin manyan abubuwan da wannan sabuwar tawagar ta sanya a gaba.

“Yana da matukar muhimmanci yadda za mu kara azama, ba gwiwarmu ta yi sanyi ba, mu da kawayenmu na yankin, mu sanya Isra’ila da kasashen yankin Gulf,” kamar yadda Antony Blinken ya nema, wanda ake sa ran za a nada sakataren harkokin wajen kasar idan majalisar dattawa ta amince.

Mista Blinken, wanda ya yi aiki da Obama da Biden a baya, ya jaddada cewa sabuwar yarjejeniyar za ta iya kawo karshen ayyukan Iran da ba su kamata ba a yankin, da kuma kokarinta na samar da makami mai cin dogon zango – karin wasu damuwa biyu da suka kamata a tattauna da kasashen yamma. Bugu da kari gwamnatin Biden ba za ta so a shure yarjejeniyar 2015 ba wadda ake kallo a matsayin wata gagarumar nasarar.

Bayanan hoto,
Amurka da kawayenta suna son kawar da shirin Iran na kera makamashin nukiliya

“Idan ka dubi wadanda Biden zai nada a matsayin jami’an harkokin kasashen waje, da maganar daina samar da nukiliya da kuma harkokin baitul malin kasar, da yawa da su aka yi maganar nukiliya a baya, wasu kuma da su aka sanya hannu kan yarjejeniyar,” in ji Ellie Geranmayeh, mataimakiyar darakta kan harkokin yankin Gabas ta Tsakiya da Arewacin Afrika a hukumar Tarayyar Turai kan harkokin kasashen ketare.

Tun bayan ficewar Amurka daga yarjejeniyar, Tehran ke nesa-nesa daga wannan yarjejeniyar ta samar da makamin nukiliya. Sanarwar da ta yi a baya-bayan nan cewa za ta koma aikin samar da makamin nukiya zuwa kashi 20 cikin 100 – sama da iyakar da aka amince mata.

Shugabannin Iran sun sha maimaita cewa za su koma kan yarjejeniyar matukar Amurka ita ma ta koma. Amma matsalolin cikin gida da suka rika tasowa ba tare da an shirya musu ba cikin shekaru hudun da suka gabata sun kara ta’azzara al’amura.

Sabuwar gwamnatin za ta fuskanci wasu hasashen cikin gida. Sabuwar majalisar Amurkan da ke cike da tsofaffin jami’an harkokin waje ta ce tana bukatar abubuwa su gyaru a Gabas ta Tsakiya wanda hakan ke nufin komai da zai fito daga Iran za a yi shi kan yarjejeniyar ne, kawo karshen sojojin Saudiyya da ke taimaka wa a yakin Yemen, dakarun zaman lafiya na hadin gwiwar da Saudiyya ke jagoranta, da kuma maganar kare hakkin dan adam a Saudiyya, ciki har da maganar tsare wadanda ake zargi da kashe dan jaridar nan Jamal Khashoggi.

Bayanan hoto,
Shugaban Iran Hassan Rouhani ya ce shirin Mr Trump’ na “matsa wa kasata lamba” bai yi nasara ba

An tambayi daraktar ma’aikatar leken asiri ta sabuwar gwamnatin Biden, Avril Haines, maganar bin doka da kuma gabatar da rahoton kisan gillar da aka yi wa Khashoggi da ake zargin wasu jami’an Saudiyya da yi a ofishin jakadancin kasar da ke Istanbul a watan Oktobar 2018.

Sai ta kada baki ta ce: “Kwarai kuwa, za mu yi aiki da doka.”

Kamar yadda wasu rahotannin sirri suka bayyana ma’aikatar tsaro ta CIA na da tabbacin Yarima Mohammed bin Salman mai jiran gado shi ya ba da umarnin a yi wannan kisa. Sai dai ya sha musanta wannan zargi.

Bayanan hoto,
Saudi yya ta yi watsi da zargin da ake yi Yarima mai jiran gado kan kisan Jamal Khashoggi

Akwai wasu manyan abubuwa da aka sanya a gaba, ciki har da kawo karshen yakin Yemen. Amma kamar ko wane irin batu shi kan shi wannan ba abu ba ne mai sauki.

“Ba sauki ba ne da shi kamar kawo karshen taimakon sojin Saudiyya,” kamar yadda Salisbury, wani babban mai sharhi na kasar Yemen da ke aiki da kungiyar da ke bibiyar rikice-rikice ta duniya, ya ja kunne. “Idan Amurka na son samar da zaman lafiya a nan, ya kamata ta kara zama mai ruwa da tsaki kan diflomasiyya.”

Diflomasiyyar za ta hada da samar da sauye-sauye na gani na fada, musamman idan wannan gwamnatin ta sanya kare hakkin dan adam cikin manyan abubuwan da ta sa a gaba. Wanda hakan ke nufin wani lamari mai wuyar sha’ani a ko ina cikin kasashen Saudiyya da Iran da Masar da sauran kasashen. Da yawa za su kagu domin ganin yadda za a aiwatar da wannan magana.

Bayanan hoto,
Gwamnatin Trump ta sasanta Isra’ila da wasu kasashen Larabawa

Kammala wasu kasuwanci da kawo karshen yake-yaken Iraki da Syria da kuma na Falasdinawa da Isra’ila, ga sabon kalubalen da ake fuskanta a Lebanon; kawo karshen barazanar al-Qaeeda da kuma IS ba karamin aiki ba ne ga gwamnatin da take fuskantar nata matsalolin na cikin gida.

“Ina ganin dole za a samu wani lokacin da zai dace,” in ji Kim Ghattas. “Zai yi matukar ba da wahala. Amma akwai lokacin da Amurka za ta sake tunani a kan rawar da za ta iya takawa a duniya da kuma Gabas ta Tsakiya.”

More News

An kashe kwamandan soji a Katsina

An kashe kwamandan sojoji na wani sansanin soji da ke Sabon Garin Dan’Ali a karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina a wani harin kwantan...

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...

Yadda rikici a kan gishirin N20 ya yi sanadiyyar mutuwar wani mutum a Kano

Wani magidanci mai suna Zakari Hamza mai shekaru 45, ya gamu da ajalinsa a hannun kanen matarsa, wani Magaji Salisu saboda gishirin N20. Dan marigayin,...