Jirgin Rasha ya yi batan dabo a teku

Jirgin ya bata ne a hanyarsa ta komawa sasanin Rasha da ke arewa maso yammacin Syria.


Jirgin ya bata ne a hanyarsa ta komawa sasanin Rasha da ke arewa maso yammacin Syria.

Wani Jirgin binciken dakarun Rasha ya yi batan dabo a tekun Mediterranean dauke da sojojin ta 14.

Kafar yada labaran Rashar ta ce kamar yadda ma’aikatar tsaron kasar a Moscow ta shaida, jirgin ya bata ne a hare-hare da Isra’ila ta kai ta sama akan Syria.

Kuma jirgin Rashar ya gano wata roka da aka harba daga jirgin ruwan yakin Faransa.

Wani jami’in Amurka da ba a bayyana sunansa ba, ya shaidawa kamfanin dilancin labaran Reuters cewa Washington na ganin cewa gwamnatin Syria ce ta kakkabo jirgin da makamin artilary amma a bisa kuskure, a kokarinta na harba makami mai linzami a kan Isra’ila.

Wannan al’amari na zuwa ne adaidai lokacin da Rasha da Turkiya suka amince su kafa yankin tudun mun tsira tsakanin dakarun gwamnati da na ‘yan tawaye a lardin Idlib na Syria.
Moscow ta ce yarjejeniyar na nufin gwamnatin Syria a yanzu za ta dakatar da kaddamar da hari a yanki na karshe da ‘yan tawaye ke da karfi wanda kuma ke dauke da mutum miliyan 3.

Rasha ta ce za a bukaci kungiyoyin da ta kira masu tsautsauran ra’ayi irinsu Al-qaeda janyewa daga yankin.

More News

Yawan Mutanen Da Suka Mutu A Wutar Da Wani Matashi Ya Cinnawa Wani Masallaci A Kano Sun  Karu Zuwa 16

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce yawan mutanen da suka mutu sakamakon wutar da wani ya cinnawa wani masallaci a ƙauyen Gadan a...

An fara rushe wasu gine-gine 500 a kasuwar Karmo dake Abuja

Hukumar FCTA dake kula da birnin tarayya Abuja ta fara rushe gine-gine sama da 500 da aka yi ba bisa ka'ida ba a kasuwar...

Tinubu ya tarbi shugaban kasar Senegal Bassirou Faye a fadar Aso Rock Villa

A ranar Alhamis ne shugaba Bola Tinubu ya tarbi shugaban kasar Senegal Bassirou Faye a fadar Aso Rock Villa, a ziyarar da Faye ya...

NEMA ta karɓi ƴan Najeriya 150 da aka dawo dasu gida daga ƙasar Chad

Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Ƙasa NEMA ta ce ta karɓi ƴan Najeriya 150 da aka dawo da su bayan da su ka maƙale...