Jiragen Yakin Najeriya Sun Isa Sokoto

Biyo bayan umarnin da shugaba Muhammadu Buhari ya baiwa mayakan Najeriya na gaggauta kawo karshen aika-aikar da ‘yan bindiga ke yi a jihar Sokoto, tuni manyan jiragen yakin sojin saman kasar suka isa jihar.

Kakakin rundunar mayakan saman Najeriya, Air Commodore Ibikunle Daramola ya shaidawa VOA cewa har ma babban Hafsan saman, Air Marshall Sadique Abubakar ya je jihar inda ya duba yadda ake tsara kai farmakin.

Daramola ya ce Babban Hafsan ya duba wuraren da jiragen yakin za su dinga shan mai don fara kai farmakin sannan ya gana da manyan kwamandojin da za su jagoranci kai farmakin.

Wasu daga cikin sakkwatawa da wakilinmu ya zanta da su sun nuna farin ciki da wannan mataki tare da fatan za a gaggauta karya lagon ‘yan ta’addan cikin gaggawa.

“Yanzu muka tabbatar da cewa ana yi da gaske don muna ta ganin yadda jirage ke shawagi.” In ji Magajin garin Gobir , Alhaji Garba Umar Kamba wanda ya nuna farin cikinsa.

A cikin farkon shekarar nan kawai mutane da dama sun rasa rayukansu a jihar saboda yawaitar kai hare-hare da ‘yan ta’adda ke yi a kwannakin nan.

More News

Gwamnan Kano ya sanya hannu kan dokar yin gwajin lafiya kafin aure

Gwamnan jihar Kano, Engr Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan wata doka za ta tilastawa masu yin aure yin wasu gwaje-gwajen lafiya gabanin...

An kashe kwamandan soji a Katsina

An kashe kwamandan sojoji na wani sansanin soji da ke Sabon Garin Dan’Ali a karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina a wani harin kwantan...

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...