Jiragen ƙasa za su fara aiki da daddare a Najeriya

Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen kasa ta Najeriya ta kammala shirin fara gudanar da ayyukan dare kafin karahen watan shida na shekarar 2024.

Manajan Darakta na NRC, Fidet Okhiria, ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da kamfanin dillancin labarai na Najeriya a ranar Litinin.

Ya fara da cewa, “Abin da ya takaita mana ayyukanmu shi ne aikin dare, kuma ba haka ya kamata jiragen kasa su rika aiki ba. Jirgi ana so yana aiki ne a kowane lokaci. Mutane na iya son yin tafiye-tafiye da yamma, amma saboda yanayin tsaro a kasar, sai mu takaita da rana.

“Muna da niyyar dawo da fasinja da jiragen dakon kaya daga Fatakwal zuwa Aba, Legas zuwa Kano, da kuma Kaduna saboda tashoshi kan tudu,” in ji Okhiria.

More from this stream

Recomended