Jihohi 30 Da Abuja Za Su Fuskanci Barazanar Ambaliya a Daminar 2025 — Gwamnatin Tarayya



Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bayyana cewa ana sa ran mamakon ruwan sama a bana zai haddasa ambaliyar ruwa a jihohi 30 da kuma birnin tarayya Abuja.

Ministan albarkatun ruwa, Farfesa Joseph Utsev, ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis yayin gabatar da hasashen ambaliyar ruwa da hukumar kula da rafuka ta ƙasa, NIHSA, ta fitar.

Cikin jihohin da aka ambata akwai Legas, Ogun, Abia, Ondo, Adamawa, Akwa Ibom, Anambra, Bauchi, Benue, Borno, Bayelsa, Cross River, Delta, Ebonyi, Edo, Gombe, Imo, Jigawa, Kebbi, Kogi, Kwara, Nasarawa, Neja, Osun, Oyo, Rivers, Sokoto, Taraba, Yobe, Zamfara, da kuma babban birnin tarayya, Abuja.

Ministan ya bayyana cewa wasu sassan yankin kudu maso kudu na iya fuskantar ambaliya sakamakon cikar tafkuna da rafuka da ruwa. Jihohin Bayelsa, Cross River, Delta, da Rivers na daga cikin wuraren da wannan matsala za ta fi kamari, yayin da Akwa Ibom da Edo ke cikin mummunan hadari.

A cewarsa, “Ambaliyar ruwa ita ce babbar masifar yanayi da ke shafar rayuwar al’umma da albarkatun kasa a Najeriya. Sauyin yanayi na kara tsananta yawan ambaliyar da ake fuskanta.”

Farfesa Utsev ya kara da cewa Abia, Benue, Legas, Bayelsa da Rivers na cikin jihohin da za su fuskanci barazana ta ambaliya a bana.

More from this stream

Recomended