Gwamnatin jihar Kwara ta karbi motocin tirela biyu cike da shinkafa buhu 1200 daga gwamnatin tarayya.
Buhunan shinkafar wani bangare ne na kokarin gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu na rage radadin da ake fuskanta a kasarnan sanadiyar cire tallafin man fetur.
Gwamnatin jihar ta ce har yanzu tana jiran kawo karin motocin uku daga gwamnatin tarayya a cewar sanarwar da gwamnatin ta fitar.
Tun bayan cire tallafin man fetur ne dai gwamnatin tarayya tayi alkawarin fitar da wasu tsaruka da za su rage raɗaɗin cire tallafin ga yan kasa.