Jihar Enugu Zata Kashe $50 Miliyan Don Samar Da Ruwa

0
Manajin darakta na hukumar samar da ruwan sha ta jihar Inugu Injiniya Martins Okwor ne ya bayyana hakan a wata zantawa da Muryar Amurka, a yayin da yawancin unguwanni a birnin na ci gaba da fama da karancin ruwan fanfo.

Ya ce, “Gwamnatin jihar ta tanadi kimanin dala miliyan hamsin don gudanar da aikin a birnin Inugu, kuma ma’aikatar kudi ta tarayya ta bada tabbacin hakan. Aikin ya kasu kashi biyu.”

Samar da ruwan sha a Inugu
Samar da ruwan sha a Inugu

Na farko ya kunshi sauya fasalin ma’aikatar ruwa, da kuma horar da ma’aikata. Na biyu kuma ya kunshi inganta kayayyakin aikin samar da ruwa, da inganta tsarin shimfida bututan ruwa, da kuma rabar da ruwa.”

Manajin daraktan dai ya ce samar da isasshen ruwan sha zata jibinci gyara aikin ruwan garin Oji River wanda ke samar wa jihar fiye da kubik mita dubu hamsin da biyar (55,000) na ruwa, da kuma gyara ma’aikatar tsabtace ruwa da ke garin Ajali mai samar da kubik mita dubu saba’in da bakwai (77,000).

Samar da ruwan sha a Inugu
Samar da ruwan sha a Inugu

Ya kuma kara da cewa za a shimfida bututun ruwa mai tsawon kilomita 12 da zarar an fara ayyukan ruwa na Oji River da Ajali.

Sai dai jama’a da dama na ci gaba da bayyana shakku kan gaskiyar lamarin, ganin an dade gwamnitoci na yin wannan alkawarin ba’a cikawa.

A cewar wani mazauni Mista Kelvin Ezendiokwere, “Kashi casa’in da biyar cikin dari na mazauna basu da ruwan fanfo, da yasa a lokacin da aka samu matsalaR mutane na cewa ai yarjejeniyar su da gwamnati ita ce idan aka gama gina gida zata samar da ruwan fanfo, amma basu ga komai a kasa ba. Toh ka ga gwamnati bata cika alkawari ba.”

Inji Mista Ike Ikechukwu, “Tun shekaru bakwai da suka wuce ne na tare a wannan unguwar, kuma ban ga ruwa a gida na ba. Saboda haka, ban ga yadda samar da ruwan zai kasance ba, saboda an sha yi mana alkawari ba a cika ba.”

Yanzu daga wannan zunzurutun kudin da gwamnatin jihar Inugu zata kashe, manajan darakta na hukumar samar da ruwan sha ya ce an riga an ware kimanin Yuro miliyan 11 da sama da Nera miliyan 300 don aiwatar da aikin ruwan garin Oji River, a yayin da wasu mazaunan na dako su ga gwamnati ta bi magana da aiki.