Jarumin Nollywwood, Mr. Ibu, ya rasu

Jarumin Nollywood, John Okafor, wanda aka fi sani da “Mr Ibu”, ya rasu yana da shekaru 62.

Emeka Rollas, shugaban kungiyar Actors Guild of Nigeria, AGN, ya bayyana hakan a shafinsa na instagram a ranar Asabar.

Mista Rollas ya ce: “Ranar bakin ciki ga ‘yan wasan kwaikwayo na Najeriya. Kate Henshaw ta rasa mahaifiyarta a safiyar yau sannan kuma Mista Ibu ya kamu da bugun zuciya a cewar manajansa mai shekaru 24, Mista Don Single Nwuzor.

“Ina mai bakin cikin sanar da ku cewa Mista Ibu ya riga mu gidan gaskiya. Allah ya jikansa ya huta.”

Idam ba a manta ba, Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya bayar da rahoton cewa a watan Oktoban 2023 cewa, John Okafor, ya bayyana cewa yana fama da rashin lafiya da ke barazanar yanke kafarsa daya.

More from this stream

Recomended