Jimillar Janar-Janar 9 a rundunar sojin Najeriya ne sun yi ritaya daga aiki.
Janar-janar din, wadanda suka fito daga sashin kudi na rundunar, su ne Maj. Gen. A.O. Adetayo, Maj. Gen. J.E. Jakko, Maj. Gen. A. R. Bakare, Maj. Gen. A. B. Adamu, Brig. Gen. N.L. Isama, Brig. Gen. O. F. Ohunyeye, Brig. Gen. O.A. Adenuga, da Brig Gen II Adamu.
Murabus din janar-janar guda tara ɗin na zuwa ne kasa da wata guda bayan da wasu janar-janar 113 suka yi murabus daga aikin sojan Najeriya a ranar 19 ga watan Disamba, 2023.
Wata sanarwa da Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Manjo Janar Onyema Nwachukwu ya fitar a ranar Lahadi ta ce an gudanar da faretin girmamawa domin karrama manyan hafsoshin a ranar Juma’a.