Jamus ta yi kakkausan gargadi ga masu juyin mulkin Nijar

Gwamnatin Jamus ta yi wani kakkausan gargadi ga masu juyin mulkin jamhuriyar Nijar da kada su yi wani abu ga shugaba Mohamed Bazoum da ake tsare da shi.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ya bayyana haka ne a birnin Berlin ranar Litinin.

“Ina son sake jaddadawa a wannan lokaci sakonmu ga masu juyin mulki cewa dole ne su yi tsammanin mummunan sakamako idan wani abu ya faru ga zababben shugaba Bazoum da iyalansa,” in ji kakakin.

“Za mu fahimci cewa a matsayin ɓata guri ne, haka ma takwsrorinmu na Afirka.”

Kakakin ofishin na harkokin wajen ya ce takunkumi da kuma gurfanawa a ciki da waje abu ne mai yiyuwa a matakan da za a dauka idan aka dauki matakin tashin hankali kan shugaban da ake tsare da shi.

More from this stream

Recomended