Jam’iyyar NNPP a Kano na Allah wadai da kalaman shugabannin APC

Hakan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da Jam’iyyar NNPP ke korafin cewa, ‘yan sanda na kallo ana raunata ‘ya’yanta a wasu sassa na birnin Kano.

A ranar Juma’ar da ta gabata ne aka jiyo shugaban Jam’iyyar APC na Kano Alhaji Abdullahi Abbas a yayin taron kaddamar da gangamin kamfe na gwamnan Kano da sauran ‘yan takara da aka yi a garin Gaya yana cewa, ko ta halin kaka sai sun ci zabe.

Yace “ina tabbatar muku wannan karon zabe…. Ance in daina fada, amma ko da tsiya ko da tsiya-tsiya, ko ana ha-maza-ha-mata, ko me za’a yi, ko me zai faru, komai ta fanjama-fanjam sai mun ci zabe”

Sai dai sa’o’i kalilan da fitar wannan lafazi daga bakin shugaban jam’iyar APC na jihar Kano, Abdullahi Abbas, shi-ma takwaran sa na Jam’iyyar NNPP, Alhaji Umar Haruna Doguwa ya mayar da martani, a yayin wata ganawa da ‘ya’yan Jam’iyyar sa.

Yace “idan adashe ne, sun zuba, muma zamu zuba namu, wallahi-wallahi, ko da tsiya, ko da wacce irin tsiyar ma, sai mun ci zabe a Kano, domin babu mutumin da ya isa ….., babu wanda ya isa….”

Tuni dai Cibiyar bunkasa fasahar sadarwa CITAD masu bibiyar kalaman batanci a kafar sadarwa ta zamani da kuma musayar kalaman tunzura Jama’a a tsakanin ‘yan siyasa ta fitar da wata sanarwa game da wannan lamari, tana mai kira ga masu ruwa da tsaki a Kano, musamman jami’an tsaro su dauki mataki.

A hirr shi da Muryar Amurka, Isa Garba, babban Jami’i a cibiyar CITAD mai Ofishi a Kano ya yi bayanin cewa, “Idan aka bar wadannan kalamai su ka ci gaba, za a samu tunzuri a tsakanin magoya bayan su, shine ya sanya muka yi kira ga masu ruwa da tsaki cewa, su yi Allah wadai da irin wadannan kalamai, a lokaci guda kuma muka bukaci su Jami’an tsaro su gayyaci wadannan shugabannin na siyasa su ja hankalin su, su kuma kama su da laifin duk wata tarzoma da ka iya biyo baya sakamakon wadannan kalamai”

A nasa banagaren, Comrade Idris Ibrahim Unguwar Gini, shugaban majalisar bunkasa rayuwar matasa ta jihar Kano yace masu yin irin wadannan kalamai ba suna yi ne domin al’ummar da za a mulka ba, yana mai cewa, hakan ce ta sanya su ke kira ga Jama’a su yi hattara.

Ga alama dai wadancan laffuza sun fara tasiri a tsakanin magoya bayan jam’iyyun biyu, domin kuwa an samu wata mummunar karanbatta a tsakanin su ranar asabar, a yankin Gwale na tsakiyar birnin Kano, inda har aka jikkata wasu ‘ya’yan Jam’iyyar NNPP guda 4, lamarin da ya sanya shugaban Jam’iyyar Umar Haruna Doguwa ya zargi ‘yan sanda da hannu. Ya kuma bukaci kwamishinan ‘yan sanda na Kano ya dauki matakin da ya kamata akan DPO na Gwale da na yankin Mandawari.

More from this stream

Recomended