Jam’iyyar Boris Johnson ta lashe zaben Burtaniya | BBC Hausa

Boris Johnson

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Jam’iyyar Conservatives ta Firai minista Boris Johnson ta lashe mafi yawan kuri’un da aka kada a zabe Birtaniya aa gagarumin rinjaye, inda yanzu haka ta lashe kujeru 348, yayin da har yanzu ake jiran sakamakon wasu mazabun.

BBC ta yi hasashen cewa Boris Johnson zai sake samun nasarar koma wa fadar faraminista da rinjayen kuri’u 74.

Firai ministan ya ce nasarar za ta ba shi damar fitar da Birtaniya daga tarayyar Turai a watan gobe.

Jagoran jam’iyyar hamayya ta Labour, Jeremy Corbyn ya ce sakamakon bai yi wa jam’iyyarsa dadi ba, sai dai ba zai sake shiga zabe na gaba ba.

Jam’iyyar ta Labour ta rasa kujeru a duka fadin Arewaci da Midlands da Wales a wuraren da a 2016 suka goyi bayan ficewar Birtaniya daga Turai.

Da yake jawabin shirin karbar nasara, Boris Johnson ya ce “sun samu nasarar da ta kawo karshen fargabar dakatar da ficewar Burtaniya daga Turai.”

Shi ma da yake magana wajen kirga kuri’unsa a Islington ta Arewa inda aka sake zabarsa, Jeremy Corbyn ya ce “jam’iyyarsa ta fitpo da kundin da zai tseratar da Burtaniya dangane da ficewarta daga Turai, amma kuma wannan zabe ya sauya komai.”

Related Articles