Jam’iyar PDP a jihar Benue ta dakatar Ayu

Jam’iyar PDP reshen jihar Benue ta sanar da dakatar da shugaban jam’iyyar na kasa, Iyorchia Ayu kan zargin yiwa jam’iyyar zagon kasa.

Takardar dakatar da Ayu mai dauke da kwanan watan 25 ga Maris na dauke da sahannun mutane 12 dake shugabantar mazabar Igyorov dake karamar hukumar Gboko ta jihar inda Ayu ya fito.

A cikin wasikar shugabannin sun yi zargin cewa Ayu ya yi wa PDP zagon kasa a mazabar a lokacin zaɓuka da aka yi na 2023.

Har ila yau jam’iyyar ta zargi Ayu da kin halartar zaÉ“en gwamnoni da na yan majalisun jihohi na ranar 18 ga watan Maris.

More News

NNPCL ya sake ƙarin kuɗin man fetur

Kamfanin mai na NNPCL ya sake ƙara kuɗin man fetur a gidajen mansa dake faɗin ƙasarnan. Wannan ne karo na biyu da kamfanin yake ƙara...

Tinubu ya bada umarnin gaggauta gyara wuta arewacin Najeriya

Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana damuwarsa kan matsalar rashin wutar lantarki da ake fama da ita a yankin arewacin Najeriya. Shugaban ƙasar ya...

Sojoji sun kama É“arayin É—anyen man fetur 35 a Neja Delta

Rundunar sojan Najeriya ta ce dakarunta sun kama mutane 35 da ake zarginsu da gudanar da haramtattun matatun man fetur da kuma lalata bututun...

Majalisar dokokin jihar Gombe ta zartar da dokar kafa hukumar kula da masu buƙata ta musamman

Majalisar dokokin jihar Gombe ta zartar da kudirin dokar da zai samar da hukumar  da za ta kula da da mutane masu buÆ™ata ta...