
Jam’iyar APC ta kori tsohon gwamnan jihar Osun, Rauf Aregbesola daga jam’iyar kan zargin da ake masa na yi wa jam’iyar zagon ƙasa.
Wata wasika da jam’iyar ta fitar ranar Laraba ita tabbatar da korar tasa.
Aregbesola wanda ya riƙe muƙamin ministan harkokin cikin gida a zango na biyu na gwamnatin Buhari da ta shuɗe ya jagoranci wani tsagi na jam’iyar APC a jihar Osun.
Jam’iyar ta ce ta ɗauki matakin ne biyo bayan sakamakon kwamitin bincike da ta kafa da ya binciki tsohon minista.
Korar Aregbesola daga jam’iyar na zuwa ne yan kwanaki kaɗan bayan da tsagin nasa suka gudanar da wani taro inda suka bayyana aniyarsu ta shirin ficewa daga jam’iyar.