
Rundunar yan sandan jihar Enugu ta ce yan bindiga uku aka kashe a wani farmaki da aka kai maboyar yan ta’addar kungiyar IPOB.
A wata sanarwa ranar Juma’a, Daniel Ndukwe mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar ya ce jami’an rundunar sun yi artabu da yan bindigar a kauyen Imufu dake karamar hukumar Igbo-Eze North ta jihar.
Ndukwe ya ce an gudanar da farmakin tare da hadin gwiwar sojoji na musamman da kuma jami’an DSS a ranar 10 ga watan Agusta.
Ya kara da cewa binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa yan bindigar su ne suka kashe wasu yan bijilante a ranar 21 ga watan Yuli.
Har ila binciken ya nuna cewa yan bindigar su ne ke ta kokarin tabbatar da sai anbi dokar hana fita a yankin karamar hukumar.
An gano tarin makamai da wasu bindigogi a maboyar yan ta’addar.