Jami’an tsaro sun kashe ƴan bindiga da dama a jihar Niger

Jami’an tsaro sun samu nasarar daƙile wani hari da ƴan bindiga suka kai a Bassa dake ƙaramar hukumar Shiroro ta jihar Niger.

Ƴan bindigar  da yawansu ya kai  sama 100 sun kai farmaki ne a ranar 11 ga watan Satumba amma sai suka fuskanci turjiya daga jami’an tsaron DSS.

Jami’an tsaron DSS biyu ne suka rasa rayukansu a fafatawar da aka yi.

Ana tsaka da fafatawar ne dakarun sojan saman Najeriya suka kai ɗauki inda suka buɗewa ƴan bindigar wuta.

Gawarwakin ƴan bindiga sama da 28 aka gano bayan da ƙura ta lafa.

Bayan ƴan bindigar da aka kashe jami’an tsaron sun samu nasarar tattara makamai da dama da kuma baburan hawa.

More from this stream

Recomended