Jami’an tsaro sun ceto mata 18 da yara 5 da aka sace a Katsina

..

Jami’an tsaro a jihar Katsina sun samu nasarar ceto mata 18 da yara biyar da aka yi garkuwa da su a ƙauyen Kwayawa da ke Ƙaramar Hukumar Safana ta jihar Katsina.

A wata sanarwa da mai magana da yawun rundanar tsaro ta Najeriya John Eneche ya fitar, ya bayyana cewa jami’an Rundunar Hadarin Daji tun da farko ta samu labarin hare-hare da ƴan bindigan ke kai wa a ƙauyen Wurma da ke Ƙaramar Hukumar Kurfi ta jihar.

Sai dai sun yi arangama da ɓarayin ne bayan sun sace wasu mazauna ƙauyen Kwayawa inda dakarun suka rinƙa kai musu hari ta sama da ta ƙasa har suka yi nasarar ƙwato dabbobi 75 da ɓarayin suka sace.

Ya kuma bayyana cewa jami’an sun samu nasarar damƙe wani da suke zargi yana bai wa ƴan bindigan bayanan sirri mai suna Mohammed Saleh.

An same shi da bindiga da harsasai, kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa tuni aka miƙa waɗanda aka ceto ga iyalansu, haka kuma dabboin da aka ƙwato ga masu su.

Jihar Katsina na daga cikin jihohin Najeriya da hare-haren ƴan bindiga ya yi ƙamari.

Ko a kwanakin baya sai da wasu da ake zargin ƴan bindiga ne suka sace ɗaliban makaranta 344 a wata makarantar sakandire a Ƙanƙara, duk da cewa an samu ceto su.

Wannan lamarin ya ja hankalin ƴan Najeriya da ma wasu ƙasashen duniya musamman bayan da ƙungiyar Boko Haram ta yi iƙirarin sace ɗaliban.

More from this stream

Recomended