Jami’an gwamnatin Birtaniya fiye da 42 sun yi murabus

Ministocin gwamnati a Birtaniya sun shafe daren jiya suna ganawa da firaminista Boris Johnson a fadarsa na gida mai lamba 10 Titin Downing – domin su lallaba shi ya sauka daga mukaminsa, yayin da sauran goyon bayan da yake da shi a jam’iyyar Conservative mai mulkin kasar ke raguwa.

BBC ta gano cewa daya daga cikin makusantansa – Sakatariyar harkokin cikin gida Priti Patel – na cikin wadanda ke lallaba shi ya yi murabus.

Mista Johnson dai ya kori Michael Gove, daya daga cikin manyan ministocinsa, wanda a baya ke kare gwamnatinsa amma a yanzu ya juya masa baya.

Sam Freedman, wani tsohon mai ba Mista Gove shawara yayin da yake karamin minista na Ilimi ya bayyana mamakinsa ga yadda Mista Johnson ke mayar da martani:Bayan da mutum arba’in da biyu suka ajiye mukami, korar wani mutumin na daban yayi kama da rashin dabara. Sai dai abin mamakin shi ne ya kori Gove ne – mutumin da suka shaku kuma suka dade tare, kuma wannan alama ce ta yadda ikon Mista Boris ke kara rugujewa ta kowane bangare.Duk da ajiye mukamai da jami’an wannan gwmanatin ta Birtaniya suka yi, ciki har da ajiye mukamin da manyan ministoci biyu suka yi, Mista Johnson ya kafe cewa ba zai mika wuya ba.Sakataren kiwon lafiya Sajid Javid da sakataren baitulmali Rishi Sunak ne suka kunna wutar wannnan rikicin na siyasa bayan da suka ce sun gane firaministan ba zai iya sauke nauyin da al’ummar Birtaniya suka dora masa ba.

More News

An ji ƙarar harbe-harbe a fadar Sarkin Kano

A daren ranar litinin ne aka bayar da rahoton jin harbin bindiga a kusa da karamar fadar inda hambararren Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero,...

Ministan shari’a nason INEC ta riƙa shirya zaɓen ƙananan hukumomi

Babban lauyan gwamnatin tarayya kuma ministan shari'a, Lateef Fagbemi ya yi kira da a soke hukumar zaɓen jihohi masu zaman kansu. Da yake magana a...

Kotu ta hana Aminu Ado ayyana kansa a matsayin Sarkin Kano

Babbar Kotun jihar Kano ta hana Aminu Ado Bayero ayyana kansa a  matsayin Sarkin Kano har sai ta kammala sauraron ƙarar dake gabanta. Kotun ta...

NDLEA ta kama wani ɗan kasuwa da ya haɗiye ƙunshi 111 na hodar ibilis  a filin jirgin saman Abuja

Jami'an Hukumar NDLEA dake yaƙi da hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi  sun kama wani mutum mai suna Emmanuel Orjinze wani ɗan kasuwa akan...