Jami’an EFCC sun kai samame gidajen kwanan ɗaliban UDUS

Jami’an Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) sun kai wani samame da tsakar dare a kan gidajen kwanan dalibai na Jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sakkwato (UDUS), wanda ya kai ga kame wasu dalibai da sanyin safiyar Asabar.

Rahotanni sun bayyana cewa an kai samamen ne a yankin Kwakwalawa da Gidan Yaro, yankunan da daliban jami’a suka fi yawa a Sakkwato. 

Kamar yadda shaidun gani da ido suka bayyana, jami’an EFCC sun kai farmaki gidajen kwanan dalibai da misalin karfe 4 na asuba, inda suka damke dalibai da dama.

Wani dalibi ya ce, “Sun zo da asuba, suka shiga dakunanmu, suka fara kama mu ba tare da wani bayani ba.” 

Har yanzu dai hukumar EFCC ba ta fitar da wata sanarwa dangane da samamen ba ko kuma ta bada dalilan da suka sa aka kama su.

Lamarin dai ya yi kama da wani samamen da aka kai a watan Fabrairu a Jami’ar Fasaha ta Tarayya da ke Akure (FUTA) a Jihar Ondo, inda jami’an EFCC suka kama dalibai a wani samame da tsakar dare da ke wajen harabar jami’ar.

More from this stream

Recomended