A jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya, iyayen yaran da aka sace na can na nuna fargaba kan makomar ‘ya’yansu.
Rahotanni sun ce wasu ‘yan bindiga ne suka afka kauyen Wanzamai da ke karamar hukumar Tsafe da safiyar ranar Jumma’a inda suka yi awon gaba da yaran.
Wani mazaunin kauyen da BBC ta tattauna da shi ya ce, yawancin yaran da aka sace matasa ne ‘yan tsakanin shekaru sha wani abu zuwa 20 da haihuwa.
Kuma ‘yan bindigar sun afka musu ne bayan da suka je neman itace da kuma gyaran gona.
Mutumin ya ce ana hasashen cewa an saci yara daga 80 zuwa 100, ko da yake ya ce akwai wadanda suka manyanta a cikin wadanda aka sacen.
Mazaunin garin ya ce akwai damuwa sosai a kan lamarin, domin ya tayar da hankali kasancewar kusan ya shafi kowa, ”idan ba danka to akwai dan dan uwanka a cikin wadanda aka sacen.”
Shi ma daya daga cikin iyayen yaran da aka sace ya shaida wa BBC cewa, yaran sun je yin itace ne a lokacin da aka sace su, kuma shi ‘yarsa guda ce a cikinsu.
Ita ma wata mahaifiyar wasu daga cikin yaran ta shaida wa BBC cewa, ‘yarta guda ce a cikinsu, kuma itace ta je yi daga nan ne aka dauke ta.
Ta ce, har yanzu babu wani karin bayani da suka samu, don ba wanda ya kira su a kan su bayar da wani kudi ko akasin haka.
Matar ta ce,” Muna nan mun shiga cikin iftila’i tun da babu kwanciyar hankali, saboda ba mu san halin da suke ciki ba.”
Duk kokarin da BBC ta yi don jin ta bakin gwamnatin jihar ta Zamfara a kan lamarin ya ci tura, haka suma jami’an ‘yan sandan jihar ba su amsa kiran da BBC ta yi musu ba.
Jihar Zamfara dai na daga cikin jihohin arewacin Najeriya da ke fama da matsalar ‘yan fashin daji wadanda ke kai hare-hare cikin garuruwa da ma kauyukan jihar.
A wasu lokutan baya ga satar abubuwa kamar shanu, sukan saci mutane har ma su nemi kudin fansa.
Najeriya dai na fama da matsalolin tsaro ko da yake hukumomi sun ce suna bakin kokarinsu don magance matsalar.