Italiya na tuhumar Luiz Suarez da satar amsar jarabawar Italiyanci

Luis Suarez

‘Yan sanda a Italiya sun kai wani samame zuwa wata jami’a da ake zargi da shirya wa dan kwallon Barcelona da Uruguay jarabawar kwarewa a harshen Italiyanci.

Luiz Suarez na bukatar takardar shaidar da ke cewa ya ci jarabawar kafin ya sami damar komawa can domin buga wa wata kungiyar kwallon kafa.

Dan kwallon ya je birnin perugia a makon jiya, inda ya rubuta jarabawar da ta gwada kwarewarsa a yaren na Italiyanci, matakin da zai ba shi damar samin fasfon kasar Italiya da ya lashe jarabawar.

Luiz Suarez na cikin manyan ‘yan wasan kwallon kafa a duniya, wanda ya lashe gasar a lokuta masu dama, amma a wannan karon ya so ya lashe jarabawar da za ta ba shi damar komawa Italiya daga kungiyar Barcelona – wannan abin kuwa shi ne fasfon Italiya.

Suarez surukin Italiyawa

Matarsa dai ‘yar Italiya ce, saboda haka yana da damar ya bukaci a ba shi fasfon kasar – amma sai bayan ya ci jarabawar da aka shirya wa masu son nuna kwarewarsa a harshen Italiyanci – wanda shi ne dalilinsa na zuwa shahararriyar jami’ar Perugia.

Sai dai ziyarar tasa ta haifar da wani samamen ‘yan sandan Italiya wadanda suke tuhumar cewa jami’ar ta ba shi satar amsa, har ma ta shirya yawan makin da za ta ba shi tun kafin ya rubuta jarabawar.

Wannan matakin ya sa ‘yan sanda na gudanar da bincike kan jami’ai biyar na jami’ar, sai dai shugabanninta sun musanta cewa jami’ar ta aikata wani laifi.

‘Yan sanda sun ce suna da bayanan sirri da suka nada na tattaunawa tsakanin malaman da ake tuhuma da masu shirya jarabawar, inda aka ji dayansu na cewa Suarez bai iya Italiyanci ba ko miskala zarratin, amma an shirya cewa za a nuna ya lashe jarabawar.

‘Yan sanda kuma na tuhumar cewa an rage tsawon lokacin da yake bukata na neman fasfon wanda ya kai tsakanin shekara biyu zuwa hudu. A madadin haka sai aka rage shi zuwa kwana 15.

Wannan binciken zai bayyana ko wannan karon Suarez ba zai ci wannan damar da ya samu ba – ba kamar yadda ya saba zura kwallaye a-kai-a-kai a filin kwallo ba.

More from this stream

Recomended