ISWAP ta kashe sojojin Najeriya shida a Borno

Mayaƙan Boko Haram

Bayanan hoto,
An jikkata wasu kusan 12 yayin harin

Aƙalla soja shida ne suka mutu sakamakon hari da mayaƙan ƙungiyar Islamic State West Africa Province (ISWAP) wadda ta ɓalle daga Boko Haram ta kai musu ranar Asabar a Jihar Borno.

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a ƙauyen Burimari lokacin da tawagar sojojin ke kan hanyarsu ta zuwa Baga, inda dakarun ƙungiyar suka yi musu kwanton-ɓauna.

Wani mai magana da yawun rundunar sojan Najeriya ya shaida wa wakilin BBC Ishaq Khalid cewa suna buƙatar lokaci domin sanin abin da ya kira “gaskiyar lamarin”.

Majiyoyi da dama, ciki har da wani soja da ya tsallake rijiya da baya, sun faɗa wa BBC cewa aƙalla soja shida ne da kuma wani mayaƙin sa-kai suka mutu a harin tare da jikkata kusan 12.

Kazalika rahotanni sun ce ‘yan bindigar sun ƙwace motar sojoji guda biyu.

Gwamnan Borno Babagana Umara Zulum ya shafe ranakun Asabar da Lahadi a garin na Baga, har ma wasu rahotanni suka ce an kai wa tawagarsa hari. Sai dai gwamnatin jihar ta musanta rahoton.

Gwamna Zulum ya je Baga ne domin ganin yadda aikin raba kayan tallafin abinci yake tafiya ga mutanen da suka koma ba da daɗewa ba bayan hare-haren Boko Haram sun raba su da mahallansu.

Yayin ziyarar aikin a Baga, Gwamna Zulum ya jagoranci raba wa mazauna yankin naira 5,000 da kayan abinci tare da duba sake gina gidajen da ‘yan bindiga suka rusa.

More from this stream

Recomended