Isra’ila da Bahrain sun kulla huldar diflomasiyya a hukumance

An shafe shekaru ba a ga maciji tsakanin kasashen larabawa da Isra'ila a gabas ta tsakiya.

Kasashen Isra’ila da Bahrain sun kulla yarjejeniyar diflomasiyya a hukumance, a wani biki da a ka gudanar a babban birnin Bahrain wato Manama a jiya Lahadi.

Yarjejeniyar wadda Amura ta samar ta kawo karshen zaman doya da manja da a ka shafe shekaru a na yi a tsakanin kasashen biyu.

An shafe shekaru ba a ga maciji tsakanin kasashen larabawa da Isra’ila a gabas ta tsakiya.

A baya kasashen sun kafe cewa ba za su shirya da Isra’ila ba har sai ta daidaita da Falasdin.

A yanzu Bahrain ta zamo kasa ta hudu a Gabas ta Tsakiya da ta maido da huldar diflomasiyya bayan kasashen Hadaddiyar Daular Larabawa da Masar da Jordan.

Ba a jima ba da a ka gudanar da irin wannan biki tsakanin Isra’ila da Hadaddiyar Daular Larabawa.

Kuma shi ne karon farko da kasashen su ka aminta da kafuwar Isra’ila tun bayan samar da ita a shekarar 1948.

To sai dai Falasdinawa sun yi tir da kasar Bahrain kan abin da ta kira ‘zamba cikin aminci’.

Jim kadan bayan kulla yarjejeniyar, ministan harkokin wajen Bahrain Abdullatif bin Al-Zayani ya ce fatan su shine ‘a samu hadin kai mai dorewa ta fuskar diflomasiyya a tsakanin kasashen biyu’.

Tun a watan da ya gabata ne Falasdin ta janye jekadan ta da ke Bahrain, bayan da ta fito fili cewa gwamnati a Manama na shirin maido da hulda da Isra’ila.

Hakama kawance ba zai yi wa Iran dadi ba, da tsoron cewa kasashen Hadaddiyar Daular Larabawa da Bahrain da Saudiyya da kuma Isra’ila a yanzu za su hade mata kai.

(BBC Hausa)

More News

Maniyyayan Najeriya sama da 18,000 sun isa Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce adadin maniyyata 18,906 na shekarar 2024/1445 aka yi jigilarsu zuwa kasar Saudiyya.Hukumar ta bayyana hakan ne a rana...

Talauci ko rashin wadata ba dalili ne na ƙazanta ba

Daga Aliyu M. AhmadBa tilas sai ka sanya manyan shadda ko yadi ba, ka É—inka daidai da kai, kilaritarka ta sha gugar charcoal. Sutura...

Ćłan sanda sun kama wani gawurtaccen mai garkuwa da mutane a Kaduna

Jami'an Ć´an sanda sun samu nasarar kama wani gawurtaccen mai garkuwa da mutane a jihar Kaduna. Mutumin da aka kama mai suna, Muhammad Bello É—an...

An yi zanga-zanga a fadar shugaban ƙasa da majalisar ƙasa kan dawo da Sarki Sanusi

Wasu masu zanga-zanga sun yi jerin gwano ya zuwa ƙofar fadar shugaban ƙasa da kuma majalisar dokokin ta tarayya kan dawo da Sarki Muhammadu...