Iran ta sha alwashin karya takunkuman Amurka

An Iranian protester burns a US banknote

Shugaban Iran Hassan Rouhani ya sha alwashin “karya” jerin takunkuman da Amurka ta sake kakaba wa kasar da zummar durkusar da tattalin arzikinta.

Gwamnatin Shugaba Donald Trump ta sake sanya wa Iran dukkan takunkuman da aka janye mata lokacin yarjejeniyar da za ta kai ta ga daina keta makamashin nukiliya a 2015.

Takunkuman za su haramta wa kasar fitar da mai da fitar da kayayyaki da kuma dakatar da hulda da bankuna, lamarin da zai yi wa kasar wahala ta samu masu huldar kasuwanci da ita.

Amma Mr Rouhani ya yi kakkausar suka ga Amurka, yana mai cewa Iran “za ta ci gaba da csayar da fetur dinta.”

“Za mu karya takunkuman da suka sanya mana,” in ji shi, a wurin da ya yi da jam’an kula da tattalin arziki.

Kasashen Turai wadanda ke cikin yarjejeniyar janye wa Iran takunkuman sun ce za su ci gaba da gudanar da huldar kasuwanci da ita da niyyar hana takunkuman yin tasiri. Sai dai ba a san hanyar da za su bi domin aiwatar da wannana manufar ba.

A farkon wannan shekarar ne Shugaba Donald Trump ya janye Amurka daga yarjejeniyar ta nukiliya, wacce ya bayyana a matsayin “mafi muni da aka amince da ita”.

Yarjejeniyar ta bukaci Iran ta daina kera makamashin nukiliya yayin da za a cire takunkuman da aka sanya mata. Hukumar da ke sanya ido kan makamashin nukiliya ta duniya IAEA ta ce Iran tana biyayya ga yarjejeniyar.

Sai dai Mr Trump ya ce yana so a koma kan teburin sulhu da Iran domin sake tattaunawa kan batun.

Mr Trump ya dauki mataki tsattsaura a kan Iran fiye da Barack Obama
Gwamnatinsa ta ce tana so ta hana Iran abin da ta kira “gudanar da wasu ayyukan masu keta dokoki” cikin har da kai hare-hare a shafukan intanet da gwajin makamai masu cin gajeren-zango da kuma goyon bayan kungiyoyin masu tayar da kayar baya a yankin Gabas ta Tsakiya.

More News

Yawan Mutanen Da Suka Mutu A Wutar Da Wani Matashi Ya Cinnawa Wani Masallaci A Kano Sun  Karu Zuwa 16

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce yawan mutanen da suka mutu sakamakon wutar da wani ya cinnawa wani masallaci a ƙauyen Gadan a...

An fara rushe wasu gine-gine 500 a kasuwar Karmo dake Abuja

Hukumar FCTA dake kula da birnin tarayya Abuja ta fara rushe gine-gine sama da 500 da aka yi ba bisa ka'ida ba a kasuwar...

Tinubu ya tarbi shugaban kasar Senegal Bassirou Faye a fadar Aso Rock Villa

A ranar Alhamis ne shugaba Bola Tinubu ya tarbi shugaban kasar Senegal Bassirou Faye a fadar Aso Rock Villa, a ziyarar da Faye ya...

NEMA ta karɓi ƴan Najeriya 150 da aka dawo dasu gida daga ƙasar Chad

Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Ƙasa NEMA ta ce ta karɓi ƴan Najeriya 150 da aka dawo da su bayan da su ka maƙale...