Iran ta kai wani gagarumin harin makami mai linzami kan Isra’ila a ranar Talata, wanda ya sa kakakin rundunar sojin Isra’ila (IDF), Rear Admiral Daniel Hagari, ya yi kira ga ‘yan kasa su daina fitar da bayanai masu muhimmanci.
A wani jawabi kai tsaye a shafin X na IDF, Hagari ya jaddada muhimmancin rike bayanai game da wurare da barnar da aka yi saboda harin, don kaucewa taimakawa abokan gaba.
“Muna kira ga ‘yan kasa kada su bai wa abokan gaba wani bayani ko hoton wuraren da aka kai hari,” in ji Hagari. Ya tabbatar wa jama’a cewa ba a gano wani barazana daga Iran a sararin samaniyar Isra’ila a wannan lokaci ba.
Hagari ya kuma gargadi kan sakamakon harin makaman, yana mai cewa Isra’ila na shirin ramawa “duk lokacin da kuma duk inda muka zaba.” Ya bayar da rahoton wasu hare-hare a tsakiyar da kudancin Isra’ila, amma babu rauni, saboda irin dabi’un da ‘yan kasar suka nuna na bin umarnin hukumomi.
Kakakin IDF ya jaddada cewa, “Harin da Iran ta kai babbar barazana ce kuma mataki ne mai hatsari. Zai sami sakamako… Za mu mayar da martani duk inda, duk lokacin da kuma ta kowanne hanya da muka ga dama, bisa ga umarnin gwamnati.”
Kimanin makami 200 aka harba daga Iran, kuma sojojin Isra’ila sun samu nasarar dakile mafi yawansu. Amurka ta taimaka wa Isra’ila wajen harbo wasu daga cikin makaman da aka harbo. Yanayin dai na nan cikin taka tsan-tsan, inda Isra’ila ta yi alkawarin kare ‘yan kasarta da kuma daukar matakin ramuwar gayya kan Iran saboda wannan hari.