INEC ta sanar da ranakun zabukan 2023

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta sanar da ranakun da za a gudanar zabukan 2023.

Tun da farko dai hukumar ta sanar da cewa za a gudanar da zaben shugaban kasa ranar 23 ga watan Faburairu sai dai shugaban hukumar ta INEC, Mahmoud Yakubu ya fadawa yan jaridu cewa an sake saka sabbin ranakun zabe.

A cewarsa yanzu za a gudanar da zaben shugaban kasa da na yan majalisun tarayya ranar 25 ga watan Faburairu yayin da za a gudanar da zaben gwamnoni da na yan majalisun jiha ranar 11 ga watan Maris.

Sanar da ranakun zaben na zuwa ne kwana biyu bayan da shugaban kasa, Muhammad Buhari ya rattaba hannu kan sabuwar dokar zabe.

More News

Jihar Neja Ta Yi Rajistar Mutane 289 Da Suka Kamu Da Cutar Amai Da Gudawa, 17 Sun Mutu

Wata annobar cutar amai da gudawa a Jihar Neja ta yi sanadin mutuwar mutane 17 tare da kama mutane 289 a kananan hukumomi 11...

An ƙona sakatariyar ƙananan hukumomi 2 a jihar Rivers

Wasu da ake kyautata zaton ɓatagari ne sun ƙona wani sashe na sakatariyar ƙananan hukumomin Eleme da Ikwerre dake jihar Rivers. Ƙona ginin na zuwa...

Ƴanbindiga sun hallaka wani shugaban APC a Kebbi

Wasu ‘yan bindiga sun harbe Bako Bala, shugaban jam’iyyar APC na karamar hukumar Suru a jihar Kebbi, a yayin wani yunkurin yin garkuwa da...

Kotu ta hana VIO kamawa, tsare motoci ko cin tarar direbobi a kan hanya

Justis Evelyn Maha ta Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta bayar da umarni da ya hana Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa, wanda aka...