Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta dakatar da Kwamishinan Zabe na Adamawa Hudu Yunusa Ari.
Wannan matakin na zuwa ne bayan sanarwar da Kwamishinan ya yi a ranar Lahadin da ta gabata bayan zaben da aka gudanar a Adamawa.
Ari ya ayyana Aisha Dahiru Binani ta jam’iyyar All Progressives Congress, APC, a matsayin wadda ta lashe zaben duk da cewa jami’an tattara sakamakon zabe ne kadai aka ba su izinin yin hakan.
Wata wasika da ta fito 17 ga Afrilu, 2023, mai dauke da sa hannun Sakatariyar INEC, Rose Oriaran-Anthony, ta sanar da dakatar da Ari tare da umurtar Sakataren Gudanarwa na Adamawa ya maye gurbinsa.