Ina Fargabar Ranar Da Talaka Zai Hambarar Da Gwamnatin Najeriya, Inji Dino Melaye

Dino Melaye, dan majalisar dattijai mai wakiltar al’ummar Kogi ta tsakiya, ya ce yana tsoron ranar da talakawan Najeriya za su fara yiwa shugabanni bore saboda yadda shugabanni ke azabtar da su.

Melaye, ya wallafa wannan furuci ne jiya a shafin sa na Tweeter, inda yace “Ina tsoron irin daukar fansa da talaka zai yi a Najeriya, irin haka ya faru a kasashen Rushiya, Faransa da kuma na kwana-kwanan nan a kasar Sudan”

“Kuma hakan ya faru ne sakamakon rashin adalcin da shugabannin kasashen ke yiwa talakan kasar, mu ma yanzu a Najeriya an kamo hanya” inji shi.

More from this stream

Recomended