Ilimin ‘ya’ya mata: ‘Rashin kayan makaranta ne ya hana ni karatun boko’

Bayanan bidiyo,
Bidiyo: Yadda talauci ya hana wata yarinya zuwa makaranta a Kebbi

Talauci na daga cikin manyan dalilan da ke hana yara mata yin karatun boko a fadin duniya, musamman a kasashe na nahiyar Afirka, baya ga al’ada da kuma wasu dalilan addini da iyaye kan dogara da su.

Wannan matsala ta rashin zuwa makarantar yara mata ta yi kane-kane a arewacin Najeriya.

Jihar Kebbi da ke arewa-maso-yammacin Najeriyar na daga cikin inda ake fama da wannan matsala, duk kuwa da cewa gwamnatin jihar ta ce tana bakin kokarinta wajen tallafa wa ilimin yara mata.

BBC ta kai ziyara jihar, inda muka tattauna da wata yarinya wadda talauci ya yi sanadiyyar lalacewar karatunta tun tana ‘yar karama.

A cewarta “Na so na yi makaranta amma hakan bai yiwu ba.”

Ubaida ta ki yin karatu ne ba don ba ta son yin karatun ba, sai dai ta bar makaranta ne saboda a cewarta ba ta da yadda za ta yi.

Ta ce “An sa ni makarantar firamare duk da cewa ba mu da karfi. Lokacin da aka sanya ni (makaranta) ba a yi min kayan makaranta ba, sai malamai suka rinka yi min fada suna bugu na saboda ba ni da inifam, kuma a lokacin ba mu da zarafi, daga nan sai na ji tsoro ban sake komawa makarantar ba.”

Yanzu haka dai Ubaida ta kai shekara 18, kuma tun lokacin da ta bar makaranta bayan da mahaifiyarta ta gaza dinka mata kayan makaranta har yau ba ta sake komawa boko da sunan karatu ba.

Duk da cewa yanzu ma takan je makarantar a kowace rana, to amma tana zuwa ne ba domin ta yi karatu ba, sai dai domin ta sayar wa dalibai Awara (kwai-da-kwai).

Yanzu haka Ubaida ta ce babu abin da ta sanya a gaba sai tallar Awara saboda ta samo kudin da za ta rufa wa mahaifiyarta da kannenta asiri.

Yadda kudin P.T.A ke hana yara karatu a jihar Kebbi

Gwamnatin jihar Kebbi dai ta ce ba ta karbar ko kwabo daga hannun iyayen yara a makarantun gwamnati. Amma kudin da ake hadawa na kungiyar iyayen yara da malamai, wanda aka fi sani da P.T.A da alama yana daya daga cikin dalilan da ya sanya wasu yaran ba su iya zuwa makaranta.

Wata mata mai yara hudu, wadda babbar diyarta mai suna Aisha take tallar Awara da soyayyen Dankali ta ce a kan koro yara daga makaranta saboda ba su biya kudin P.T.A ba.

Ta ce “Shekaran-jiya aka koro yara a kan kudin P.T.A, kuma aka ce duk wanda bai biya ba kada ya koma, ga shi yanzu komai ya yi tsada, abinci za a ba su ko kuwa kudin makaranta? Sai muka ce su yi zaman su kawai.”

Zaki Muhammad Sani wani mahaifi ne “Akwai wani abu da malamai ke yi, idan yaro bai zo da kudin P.T.A ba sai su zane shi, to shi yaro idan ya dubi wannan sai ya ki zuwa makaranta.”

Me gwamnatin jihar Kebbi ke cewa?

Kwamishinan ilimi na matakin farko da na biyu a jihar Kebbi shi ne Muhammad Magawata Aleiro, ya ce ba talauci ne kawai ke sa mutane su ki sa yaransu a makaranta ba.

“A nan Kebbi ba a biyan ko kwabo, idan ka ga yaro ya biya kudi to ‘yan kungiyarsu ne na P.T.A.” in ji Muhammad Magawata.

Ya ce jihar Kebbi na da makarantu saba’in wadanda ta ke ciyar da dalibai sau uku a kowace rana.

Ya kuma kara da cewa gwamnatin jihar tana kula da makarantun mata na kwana da na je-ka ka dawo, ta yadda iyaye ba za su kashe kudaden ciyarwa ko dawainiyar zirga-zirgarsu zuwa makarantar ba. Haka nan kuma ya ce gwamnatin na son ta tabbatar da cewa kowace yarinya ta yi karatu akalla zuwa mataki na karamar sakandare.

Wani rahoto na asusun kula da yara na majalisar dinkin duniya ya ce akalla yara mata miliyan dari da talatin da biyu ne ba su zuwa makaranta a fadin duniya.

Talauci da auren wuri da yake-yake da kyamar karatun Boko na gaba-gaba wajen hana yara mata karatu a sassa daban-daban na duniya, musamman ma a kasashe masu tasowa kamar Najeriya.

Wannan rahoto ne da BBC Hausa ta kawo maku tare da tallafin gidauniyar MacArthur.

More News

Yadda rikici a kan gishirin N20 ya yi sanadiyyar mutuwar wani mutum a Kano

Wani magidanci mai suna Zakari Hamza mai shekaru 45, ya gamu da ajalinsa a hannun kanen matarsa, wani Magaji Salisu saboda gishirin N20. Dan marigayin,...

Sojoji Sun Kashe Mayaƙan IPOB 5

Dakarun rundunar sojan Najeriya da kuma ta rundunar sojan ruwan Najeriya a ranar Talata sun kashe mayaƙan ƙungiyar IPOB guda biyar a yayin musayar...

ĆŠan agajin Izala ya samu lambar yabo, kujerar hajji, kyautar mota bayan ya tsinci naira miliyan 100 ya mayar wa mai su

Salihu AbdulHadi Kankia, mamba ne na kungiyar agaji ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatus Sunnah (JIBWIS), ya samu yabo da tukuicin mayar da...

Musulmi a Zaria sun yi taron addu’o’i saboda mummunan halin matsi da Najeriya ke ciki

Musulmi a garin Zaria na jihar Kaduna, sun gudanar da addu'a ta musamman domin neman taimakon Allah kan halin da 'yan Najeriya ke ciki...