Idan ba a taka wa Iran burki ba, duniya za ta shiga rudu – Yariman Saudiyya

Getty Images
Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Yarima mai jiran gado na Saudiyya ya yi gargadin cewa farashin mai zai iya tashin gwauron zabbi idan kasashen duniya ba su yi wani abu kan Iran ba.

Mohammed bin Salman ya bayyana cewa rikicin da ke tsakanin Saudiyya da Iran zai janyo matsin tattalin arziki ga duniya baki daya.

Wannan na zuwa ne bayan wani hari da Saudiyya ta zargi Iran da kai wa matatun mai biyu na kasar a kwanakin baya.

Yariman Saudiyya ya ce yana da laifi wajen kisan dan jarida Jamal Khashoggi, amma kuma ya musanta cewa shi ya bayar da umarnin kashe shi.

Ana ganin Yarima Mohammed a matsayin mai karfin iko a Saudiyya, haka zalika ana zarginsa da bayar da umarnin kashe Kashoggi, wanda dan jarida ne mai yawan caccakar gwamnatin Saudiyya.

An kashe Mista Kashoggi a ofishin jakadancin Saudiyya na birnin Turkiyya a ranar 2 ga watan Oktobar bara.

Iran ta yi watsi da zargin da Saudiyya ke yi mata na kai hari a matatun manta wanda harin ya janyo tsaiko ga kashi biyar cikin 100 na samar da mai ga kasashen duniya.

Amma Yarima Mohammed ya shaida cewa ”Idan kasashen duniya ba su dauki mataki domin dakile Iran ba, za mu ga karuwar irin wadannan abubuwa da za su yi barazana ga duniya.

”Za a samu matukar tashin danyen mai da ba a taba gani ba a duniya.”

Ya bayyana cewa ”yankin Gabas ta Tsakiya ke da kashi 30 cikin 100 na makamashin da ake amfani a duniya, kuma yankin ne ke da iko da kashi 20 cikin 100 na kayayyakin da ke wucewa zuwa kasuwannin duniya.

Ya kara da cewa su ke da kashi hudu cikin 100 na yawan arzikin duniya.

Daga karshe Yarima ya shaida cewa ”ku yi tunanin duka wadannan abubuwan su tsaya cik, wannan na nufin karyewar tattalin arzikin duniya baki daya, ba wai Saudiyya kadai ba ko yankin Gabas ta Tsakiya.”

More News

ÆŠalibai a Jami’ar Jos na zanga-zanga saboda rashin wuta da ruwa

Wasu daliban jami’ar Jos da ke jihar Filato a ranar Alhamis sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da matsalar karancin ruwa da rashin...

MTN yana ƙoƙarin ƙara kuɗin kati da data a Najeriya

Katafaren kamfanin sadarwa na MTN na kokarin kara kudin katin waya da na data a Najeriya. Kamfanin sadarwa mafi girma a nahiyar Afirka ya ba...

Gwamnatin Kano Ta Rage ₦500,000 A Kuɗin Aikin Hajjin Bana

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da yiwa maniyatan Aikin Hajji da suka fito daga jihar kyautar ₦500,000 domin su cika kuɗin...

Ƴan bindiga sun sace wani limami a jihar Kogi

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da Quasim Musa babban limamin garin Iyara dake ƙaramar hukumar Ijumu ta jihar Kogi. Lamarin ya faru ne a ranar...