
Abike Dabiri-Erewa shugaban hukumar NIDCOM dake lura da yan Najeriya mazauna kasashen waje ta ce gwamnatin Misra ta buɗe kan iyakarta ga ɗaliban Najeriya da aka dauko daga Sudan.
Dabiri-Erewa ta ce an buɗe kan iyakar ne biyo bayan wayar tarho da shugaban kasa Muhammad Buhari ya yi da takwaransa na Masar, Abdulfatah El-Sisi.
Sanarwar ta NIDCOM na zuwa ne sa’o’i bayan sanarwar da hukumar ta fitar dake cewa hukumomin ƙasar Masar sun gaza buɗe kan iyakar duk da cewa jiragen rundunar sojan saman Najeriya sun isa kasar domin kwato ɗaliban.
Ta kara da cewa an bude kan iyakar ne bayan gindaya wasu tsauraran sharuɗa da bata bayyana ba.