Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta kama wasu mutane 15 da ake zargi da aikata damfarar intanet a garin Makurdi, Jihar Benue.
A wata sanarwa da hukumar ta wallafa a ranar Talata ta shafin X, an bayyana cewa jami’an hukumar na reshen Makurdi ne suka kama mutanen a unguwar Abu King Shuluwe, Akpehe, bayan samun bayanan sirri kan ayyukan damfara da ake zarginsu da aikatawa.
EFCC ta kuma bayyana cewa, an kwace kayayyaki daban-daban daga hannun wadanda ake zargin, wadanda suka hada da motoci biyu, kwamfutoci biyar, da wayoyin hannu 17.
Hukumar ta ce, “An kama wadanda ake zargin ne a unguwar Abu King Shuluwe, Akpehe, cikin garin Makurdi, bisa sahihan bayanai kan zarginsu da aikata damfarar intanet.
“Kayayyakin da aka kwace daga hannunsu sun hada da: motoci biyu, kwamfutoci biyar, da wayoyin hannu 17, da sauransu. Za a gurfanar da su a gaban kotu da zarar bincike ya kammala.”