
Hukumomin Asibitin Koyarwa na Jami’ar Usmanu Danfodiyo dake Sokoto sun ce babu wata bakuwar cuta da ta bulla a asibitin.
Shugaban asibitin koyarwar, Dr.Anas Sabir shi ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da shugaban sashen hulda da jama’a na asibitin, Mallam Buhari Abubakar ya fitar a Sokoto ranar Asabar.
Sabir ya ce karin hasken ya zama dole idan aka yi duba da wani fefan muryar wani da ba a san kowaye ba da ake yadawa a gari dake cewa wani mara lafiya da aka kawo daga jihar Kaduna ya mutu sanadiyar wata bakuwar cuta kwanaki kadan bayan an kwantar da shi a asibitin.
Ya ce mutumin da ya yi kalaman ya alakanta majiyarsa da wasu gidajen rediyo biyu dake jihar inda ya yi kirarin cewa karin wasu marasa lafiya 15 sun mutu a asibitin sanadiyar cutar.
“Domin kawar da duk wani shakku hukumomin asibiti suna so su bayyana a fili karara cewa har kawo wannan lokaci yanzu basu karbi mai wannan cuta daga Kaduna ko wani wuri a kasarnan.” a cewar sanarwar.
Sanarwar ta cigaba da cewa ikirarin da aka ji a cikin fefan muryar da ake yadawa bashi da tushe bare makama karya ce tsagwaronta.