Hukumar Kula da Gyaran Hali ta Najeriya (NCoS) ta tabbatar da kama wasu daga cikin fursunonin da suka tsere daga Kurkukun Tsaro na Matsakaici da ke Koton Karfe, Jihar Kogi.
Kakakin hukumar, Abubakar Umar, ya bayyana cewa tsagerun sun tsere ne a safiyar Litinin, 24 ga Maris, bayan wasu daga cikin wadanda ke jiran shari’a sun lalata makullin da ke rike da su, lamarin da ya haddasa arangama da jami’an tsaro.
Bayan samun rahoton faruwar lamarin, Mukaddashin Kwamturolan Hukumar NCoS, Sylvester Nwakuche, ya hada kai da hukumomin tsaro da kuma Mai Ba Gwamnan Jihar Kogi Shawara na Musamman domin tsaurara matakan tsaro a wurin tare da fara farautar wadanda suka gudu.
“A halin yanzu, mun samu nasarar cafke biyar daga cikin fursunonin da suka tsere, yayin da ake ci gaba da kokarin kama saura domin gurfanar da su a gaban doka,” in ji Umar.
Ya kara da cewa an kaddamar da bincike domin gano yadda aka samu wannan matsala, tare da yin duba na musamman ga dukkan cibiyoyin gyaran hali a fadin kasar nan domin hana irin wannan aukuwar a gaba.
Hukumar ta bukaci jama’a su kasance masu lura da duk wani abu da zai iya taimakawa wajen cafke sauran da suka tsere, tare da mika rahoto ga hukumomin tsaro idan an ga wani da ake zargi.
Hukuma Ta Kama Fursunoni Biyar Daga Cikin Wadanda Suka Tsere A Kurkukun Koton Karfe
