Hukuma a Kano ta yi barazanar kama duk wani ɗan kasuwa mai ɓoye kayan masarufi

Hukumar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano, ta yi barazanar kame kayan da aka boye tare da gurfanar da masu aikata wannan laifin a gaban kuliya.

Shugaban hukumar Muhyi Rimingade ne ya yi wannan barazanar a ranar Alhamis yayin da yake yi wa manema labarai karin haske kan hauhawar farashin kayayyaki a fadin kasar.

A cewarsa, hukumar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kwace kayayyakin da aka boye tare da gurfanar da masu laifin a gaban kuliya.

Ya yi bayanin cewa hukumar za ta dauki kwakkwaran mataki kan daidaikun mutane ko ’yan kasuwa da aka samu suna tara kayan masarufi domin a samun riba mai yawa a kai.

More News

Gwamantin Kano na kashe naira biliyan 1.2 duk wata don samar da ruwan sha—Kwamishina

Gwamnatin jihar Kano na kashe kimanin naira biliyan 1.2 duk wata don samar da ruwan sha na tafi da gidanka a cikin babban birnin...

Wasu ɗaliban Jami’ar Jihar Nasarawa sun mutu a lokacin turmutsutsin karɓar tallafin abinci

Dalibai biyu daga Jami’ar Jihar Nasarawa da ke Keffi (NSUK) sun rasa rayukansu a wani turmutsitsi da ya barke a lokacin da suke kokarin...

Jarumin Nollywwood, Mr. Ibu, ya rasu

Jarumin Nollywood, John Okafor, wanda aka fi sani da "Mr Ibu", ya rasu yana da shekaru 62. Emeka Rollas, shugaban kungiyar Actors Guild of Nigeria,...

Miyetti Allah ta nemi a cafke Sunday Igboho saboda barazanar yaƙar Fulani

Kungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria, MACBAN, ta yi kira da a damke wani dan kabilar Yarbawa, Sunday Adeyemo, wanda aka fi...