Hatsarin jirgin sama ya yi sabanin mutuwar rai hudu a Dubai

View of Dubai airport with city in background

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Mutum hudu sun mutu sanadiyar wani hatsarin jirgin sama da ya fado kimanin kilomita uku yamma da babban filin jirgin saman Dubai.

Hukumomin Hadaddiyar Daular Larabawa sun ce uku daga cikin mamatan ‘yan Birtaniya ne, daya kuma dan Afirka ta Kudu ne.

Dukkansu na cikin wani jirgin sama ne samfurin DA42.

Jirgin mai iya daukar mutum hudu mallakin kamfanin Flight Calibration Services da ke filin jirgin sama na Shoreham a yankin West Sussex na Ingila.

An fara gudanar da bincike kan dalilin wannan hatsarin.

Rahotanni daga kafafen watsa labarai na Dubai na cewa jirgin ya fado ne da misalin karfe 7:30, inda direban jirgin da mataimakinsa da kuma fasinjoji biyu dake cikin jirgin suka gamu da ajalinsu.

An rufe filin jirgin sama na Dubai har tsawon minti 45 bayan hatsarin, inda aka karkatar da akalar wasu daga jiragen sama da ke neman izinin sauka da fasinjojinsu.

More News

MTN yana ƙoƙarin ƙara kuɗin kati da data a Najeriya

Katafaren kamfanin sadarwa na MTN na kokarin kara kudin katin waya da na data a Najeriya. Kamfanin sadarwa mafi girma a nahiyar Afirka ya ba...

Gwamnatin Kano Ta Rage ₦500,000 A Kuɗin Aikin Hajjin Bana

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da yiwa maniyatan Aikin Hajji da suka fito daga jihar kyautar ₦500,000 domin su cika kuɗin...

Ƴan bindiga sun sace wani limami a jihar Kogi

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da Quasim Musa babban limamin garin Iyara dake ƙaramar hukumar Ijumu ta jihar Kogi. Lamarin ya faru ne a ranar...

Delta: An dawo da gawarwakin sojojin da aka kashe Abuja don yi musu jana’iza

Gawarwakin sojojin da aka kashe a jihar Delta kwanan nan sun isa maƙabartar sojoji ta kasa da ke Abuja. Gawarwakin sun iso ne da misalin...